Auren Zawarawa: Gwamnatin Kebbi ta sake daukar nauyin wasu 100

Auren Zawarawa: Gwamnatin Kebbi ta sake daukar nauyin wasu 100

- Gwamnatin Kebbi ta dauki nauyin Auren Jawarawa 100

- Abun farin ciki da jin dadi ga Jawarawa 100 a jihar Kebbi, tinda yanzu sun sake gidaje

- Gwamnatin jihar jiya ta daura masu aure a fadar sarkin Argungu, Alhaji Samila Mera

- Gwamnatin jihar da karamar hukumar jihar sukayi hadin gwiwa na daukar nayin auren jawarawan

Auren Zawarawa: Gwamnatin Kebbi ta sake daukar nauyin wasu 100
Auren Zawarawa: Gwamnatin Kebbi ta sake daukar nauyin wasu 100

Abun farin ciki da jindadi ya sami Jawarawa 100 a jihar Kebbi, tinda yanzu sun sake gidajen zama. Gwamnatin jihar jiya ta daurawa jawarawan aure a fadar sarkin Argungu, Alhaji Samila Mera.

Gwamantin jihar data Karamar Hukuma ta jihar ne sukayi hadin gwiwa na daukar nauyin auren jawarawan, don a rage yawan jawarawa da aka saki da wadanda mazajensu suka mutu suka barsu da yara su kula dasu.

Gwamnan jihar Kebbi, ya yabawa kokarin da Sarkin garin yayi da karamar hukuma ta garin, sannan kuma yayi kira ga iyaye dasu girmama wannan aure, don shine hanyar rage yawan mata marasa aure a garin. Ya kara yin kira ga “ma’auratan dasu cigaba da hakuri da jurewa zama da juna don samun zaman lafiya a gidajen aurensu, yana nuna musu cewa, aure hakurine da juriya a cikinsa, wanda hakan zaisa su samu lada da rahamar Allah”, inji Gwamnan.

DUBA WANNAN: Yaje Lahira ya dauko hoto ya dawo yana sayarwa 5000

Sarkin na Argungu, a jawabinsa na rufe taro, yayi jinjina ga gwamnatin jiha data karamar hukuma na hadin gwiwar da sukayi don ganin hidimar ta yiwu kamar yanda Musulunci ya tsara.

Anji cewa gwamnatin jihar ta biya N20,000 na “Sadaki” ga matan, sai kwanoni da tukane, da kofofi masu kyau, da farantai, da mayafai, wadanda sune shidar aurensu.

An kuma bawa kowace mace N30,000 domin taja jari, sannan kuma gwamnatin ta basu gudummuwar kayan daki dana kicin wanda a kalla zasu kai N150,000, ga kowane ma’aurata.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng