An aurar da zawarawa sama da 1,500 a Kano

An aurar da zawarawa sama da 1,500 a Kano

Gwamnatin jihar Kano ta aurar da zawarawa mata da maza sama da 1,500 a karshen makon da ya gabata duk a cikin shirinta da rage yawan zawarawa.

Gwamnatin jihar ce ta dauki nauyi aurar da mutanen a wani yunkuri na ragewa iyayen da ba su da karfin aurar da 'ya'yan su hidima, da kuma rage yawan marasa aure a jihar.

An aurar da zawarawa sama da 1,500 a Kano

Wannan ba shi ne karon farko da gwamnatin jihar Kano ta fara aurar da zawarawan ba, an faro wannan aikin ne tun zamanin tsohon gwamnan jihar wato Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso.

A wannan karo an zabo sama da mata da maza talatin a kowacce karamar hukuma da ke jihar, wanda kuma gwamnati ita ce ta biya kudin sadaki da kuma sanyan kayan daki ga ma'auraten.

KU KARANTA KUMA: Wasu na son Buhari ya rasu domin abasu kujeran Mataimakin shugaban Kasa – Inji Shehu Sani

An gudanar da dauren auren ne bayan da aka tantance ma'auraten ta bangaren lafiyar jikinsu da kuma hankalin su baki daya.

Wannan lamari dai na irin dauren wannan aure na sa matasa su natsu kuma ya kare su da yin zinace-zinace.

Sarkin Kano, Mallam Muhammadu Sanusi yay aba ma gwamnatin jihar Kano da ta dauki nauyin auren mata da yawan, ya kuma tabbatar da cewa kungiyar masarautar zasu ci gaba da ba duk wani shiri na gwamnati da zai taimaka wa jama’a goyon baya.

Da yake magana, shugaban kungiyar Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, yace yarjejeniyar da akayi tsakanin gwamnati da angwannan shine cewa babu wanda zai saki matarsa ba tare da izinin kungiyar ba.

Ya kuma bukaci ma’auratan da su zauna da junansu cikin zaman lafiya da amana, cewa amfanin aure dama shine a zauna cikin rayuwa mai inganci kuma cewa baza’a iya cimma wannan manufa ba idan babu zaman lafiya da amana.

Ku biyo mu: https://www.facebook.com/naijcomhausa/ da nan https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: