Mai Ciki Ta Haihu a Tsaye Yayin da Ake Cigaba da Kashe Bayin Allah a Filato
- A tsakiyar bainar jama’a wata mai tsohon ciki ta haihu a garin Mangu inda ake ta kashe-kashe a yanzu
- Wannan mata mai ‘ya ‘ya biyu ta ji nakuda ta zo kwatsam a lokacin da kowa ya tsere a garin Mangu
- Akwai wanda take shirin aurar da yaronta da ta ci karo da gawar mai gidanta bayan sun rasa komai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Plateau - Wata Baiwar Allah da aka bada sunanta a matsayin Zainab, ta haifi jariri a fili a garin Mangu da ke jihar Filato.
Sabon rikici ya sake barkewa a karamar hukumar Mangu musamman daga ranar Talata, Daily Trust ta kawo rahoton.
An haifi yaro a fili a Mangu
Zainab wanda take dauke da tsohon ciki ta bada labarin yadda ta tsure a lokacin da ta ji harbe-harben bindigogi ta ko ina.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Baya ga karar makamai, mai juna biyun ta ga yadda ake kashe mutane, kafin a ce kobo sai ta ji zugin nakuda ya zo mata.
Ana haka sai wannan mata mai shekara 25 ta ji yaro zai fado a filin Allah.
"Da na ji yaron zai fito, sai na tsuguna domin tabbatar da cewa na haifi jaririn lafiya."
"Babu agajin malaman asibiti, ko kayan aiki masu tsabta ko wurin haihuwa mai dadi.
"Wata makwabcitya ce kurum ta tsaya ta taimaka mani domin a lokacin kowa ya tsere."
- Zainab
Mangu: An tsinci gawar mai gida
Wannan mata mai rike da marayu biyar ta shaidawa jaridar yanzu babu asibiti a bude saboda dokar kullen da aka kakaba.
Wata mai suna Maryam tace ana haka ta tsinci gawan mijinta har ya fara rubewa bayan an kona gidansu da kuma shagonsu.
Wannan mata tace tana shirye-shiryen aurar da yaronta ne, aka kona masu komai.
Jama’atu Nasril Islam tayi ikirarin an kashe mata mutane akalla 13, kungiyar Mwaghavul kuwa tace ta rasa mutane har 30.
Har yanzu babu tabattaccen adadin wadanda aka rasa a sanadiyyar rikicin duk da matakin da Caleb Mutfwang ya dauka.
“Addu’a kurum za ayi mana” - Mazauni
Wata majiyar mu ta shaida mana ana zargin jami’an tsaro da son kai a maimakon su kawo zaman lafiya a yankin na Mangu.
Wani matashi yace suna kallo wani ya bindige abokinsu saboda sabanin addini duk da abokantakar da ke tsakaninsu a baya.
Da aka yi magana da saurayin, yace suna zargin ana neman kona masallacinsu kuma babu abin da suke bukata sai addu’a.
Harin Boko Haram a Borno
Ana da labari 'yan ta'addan Boko Haram sun yi wa sojoji kwantan ɓauna a jihar Borno, a dalilin haka an rasa wasu sojoji.
Miyagun sun kashe babban soja ɗaya, da wasu jami'an tsaro guda biyu a harin.
Asali: Legit.ng