Dattijo Dan Najeriya Ya Zama Biloniya, Zai Goga Kafada da Su Dangote, Adenuga a Masu Kudin Afrika
- Wani ma'aikacin banki kuma dan kasuwa, Adebayo Ogunlesi ya shiga sahun manyan attajirai a nahiyar Afirka
- Hakan na zuwa ne bayan da Ogulesi ya sayar da kamfaninsa, Global Infrastructure Partner akan kudi dala biliyan 12.5
- Da wannan sabon cinikin da ya yi, dattijon Najeriyar ya shiga sahun manyan attajirai 20 a Afrika, inda ya mallaki dala biliyan 2.3
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Wani dan Najeriya mai kamfanin Global Infrastructure Partners (GIP), Adebayo Ogunlesi ya shiga sahun attajiran Afrika bayan siyar da kamfaninsa akan dala biliyan 12.5.
Wani rahoto na Bloomberg ya bayyana cewa kamfanin Amurka BlackRock mallakin attajiri Larry Fink ne ya sayi kamfanin Ogunlesi bayan dogon lokaci ana ciniki.
Ogunlesi ya shiga sahun attajirai 20 mafi arziki a Afrika
A cewar rahotanni, an cimma matsaya kan biyan tsabar kudi har dala biliyan uku, sai kuma hannun jari miliyan 12 a kamfanin na GIPs da kudin su ya kai dala biliyan 9.5.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yanzu da ya ke da kaso 17.5% na hannun jari a GIP, Ogunlesi ya shiga sahun attajiran Afrika. Shi ne ya samar da kamfanin BlackRock a shekarar 2006.
A lokacin da ya ke shugaba, kamfanin ya zama na daya a duniya da ya shahara kan gine-gine, da darajar sa ta haura dala biliyan 100.
GIP ya mallaki filin jiragen sama na birnin Landan
Yanzu da BlackRock ya mallaki GIP, Ogunlesi ya samu babbar nasara ta fadada ayyukansa zuwa fannin sufuri, hakar ma'adanai da samar da makamashi, Premium Times ta ruwaito.
A shekarar 2006 ne GIP ya mallaki filin jiragen sama na birnin Landan, da ya daga darajar kamfanin a idon duniya.
Kamfanin BlackRock ya ce zai nada Ogunlesi matsayin mamba a kwamitin gudanarwa a zaman sa na gaba bayan mallakar GIP.
Hakan na nufin Ogunlesi da sauran mutum 4 da suka assasa GIP za su ci gaba da kula da kamfanonin biyu da zai kara fadada gudanar da ayyukansu.
An gano wadanda suka fi Elon Musk da Bill Gates arziki
A wani labarin makamancin wannan, Legit ta yi bayani kan wata zuriya a masarautar kasar Saudiyya da ta ninka arzikin attajiran duniya Elon Musk da Bill Gates da kusan kaso 4.
An ruwaito cewa zuriyar Sarkin Saudiyya ta mallaki kudi da suka kai dala tiriliyan 1.4 yayin da Musk ya mallaki dala biliyan 251.3 da kuma Bill Gates da ya mallaki dala biliyan 119.6.
Asali: Legit.ng