Jerin Masu kudin Najeriya 3 da su ka shiga sahun manyan Attajiran Afrika a shekarar 2021
- Mujallar Forbes ta fitar da sunayen manyan Attajiran Afrika a shekarar nan
- Aliko Dangote, Abdussamad Rabiu da Mike Adenuga aka samu daga Najeriya
- Abdussamad Rabiu wanda ya cika shekara 61 yau, ya ba Dala biliyan 5 baya
Afrika - Mujallar Forbes ta fitar da jerin manyan attajiran Afrika da karin bayani game da hanyar da suka bi, suka mallaki dukiyar da suka tara a Duniya.
A shafinta na yanar gizo, Forbes ta kawo sunayen masu kudin nahiyar, wanda suka shiga cikin sahun manyan masu kudin Duniya na buga wa a jarida.
Attajiran Afrika 18 ne suka iya shiga da’irar masu kudin da ake ji da su a Duniya a shekarar 2021. Sai mutum ya na da Dala biliyan 1 sannan ake maganarsa.
Kamar yadda aka saba a shekarun bayan nan, wannan karo ma Aliko Dangote ne na farko a jerin. Har yanzu ba a samu wanda ya sha gaban shi a Afrika ba.
Ragowar masu kudin Najeriya da aka ambata a wannan jeri su ne takwaron Dangote a kasuwanci, Alhaji Abdussamad Rabiu da Mike Adenuga.
1. Aliko Dangote
Mai kudin Najeriya da Afrika, Aliko Dangote ya mallaki akalla fam Dala biliyan 12.1, idan aka yi lissafi a kudinmu na gida, ya ba sama da Naira tiriliyan biyar baya.
Hanyar samun kudi: Siminti da sukari.
Shekaru: 64
2. Mike Adenuga
Mutum na biyu daga Najeriya a jeri shi ne Mike Adenuga wanda ya zo na biyar a fadin Afrika a wannan shekarar. Shugaban kamfanin na GLO ya mallaki Dala biliyan 6.3.
Hanyar samun kudi: Kamfanin sadarwa da harkar mai
Shekaru: 68
3. Abdussamad Rabiu
Attajirin karshe daga Najeriya da sunansa ya fito a sahun masu kudin nahiya, wani mutumin Kano ne, Abdussamad Rabiu mai shekara 61, yana da fam Dala biliyan 5.1.
Hanyar samun kudi: Siminti da sukari.
Shekaru: 61
Ku na da labari cewa Aliko Dangote ya na gina katafaren matatar man fetur da babu irinsa a Duniya. Matatar za ta rika tace gangar danyen mai 650, 000 a kowace rana.
A taron majalisar ministoci da aka yi na makon nan, gwamnatin tarayya ta yarda za ta saye 20% na hannun jarin matatar Dangote domin a rika tafiya da gwamnati a harkar.
Asali: Legit.ng