Filayen sauka da tashin jiragen sama 5 masu matukar kyau a Afrika
- Nahiyar Afrika ta kasance nahiyar da ta mallaki wuraren shakatawa
- Hakan yasa ta mallaki filayen sauka da tashin jiragen sama masu matukar kayatarwa
- Ana amfani da filayen jiragen saman ne wurin sauka da tashin fasinjoji zuwa wurare daban-daban
Yayin da nahiyar Afrika ta zama babban wurin shakatawa da kuma hada-hada, akwai wasu manyan filayen jiragen sama da nahiyar ke alfahari da su.
A Afrika, akwai filayen sauka da tashin jiragen sama biyar da nahiyar ke alfahari da su wurin kyau da kayatarwa, Pulse.ng ta ruwaito.
An zuba miliyoyin daloli wurin gina filayen sauka da tashin jiragen saman wanda hakan Yasa suka kasance kayatattu.
1. Filin sauka da tashin jiragen sama na Sharm El-Sheikh da ke Egypt
Wannan filin sauka da tashin jiragen saman ya kasance na farko a wannan jerin. Shine na uku a zama mafi hada-hada a Egypt bayan wanda yake a Cairo. An kaddamar da shi a 2007.
Yana da wurin da Ashe fasinja miliyan biyar a kowacce shekara. An kashe dala miliyan 350 wurin gina shi.
2. Filin sauka da tashin jiragen sama na Cape Town da ke kasar Afrika ta Kudu
Wannan shine fili na biyu idan aka duba bangaren hada-hada a kasar Afrika ta Kudu kuma na uku a Afrika. Yana da Nisan kilomita 20 tsakaninsa da birni. An kashe dala miliyan 115 wurin gina shi.
KU KARANTA: EndSARS: Mota kirar SUV ta mitsike masu zanga-zanga 4 a kan titi
3. Filin sauka da tashin jiragen sama na Marrakech Menera
Kasancewar Marrakech na daya daga cikin birane masu kyau a Afrika, babu shakka zai mallaki filin jirgin sama mai kyau. A kalla fasinja 4.5 miliyan suna shiga da fice a filin jirgin a duk shekara.
KU KARANTA: Kwamitin bincike na Salami na kokarin kakaba wa Magu laifi ta kowacce hanya - Lauyan Magu
4. Filin sauka da tashin jiragen sama na Sir Seewoosagur Ramgoolam da ke Mauritius
An kaddamar da shi a 2013 kuma an yi masa yanayin ginin siffar wata itaciya da ke fitowa a Mauritius. A kalla jama'a miliyan 4 ke hada-hada a filin jirgin a kowacce shekara kuma an kashe miliyan 306 wurin gina shi.
5. Filin sauka da tashin jiragen sama na Enfidha-Hammanet da ke Tunisia
An kaddamar da shi a 2009 kuma sau da yawa masu yawan bude ido da zuwa hutu a kasar Tunisia.
Yana da wani tsari mai matukar kayatarwa kuma ya lamushe dala miliyan 504 wurin ginin shi.
A wani labari na daban, wani babban tarihi na nahiyar Afrika da ba a iya mayewa da shi yana masarautar Benin, gari mai matukar tarihi kuma har yanzu yana daukar hankali.
An gano cewa an barar da bangon babbar masarautar a 1897, lamarin da ya matukar girgiza babban tarihin Benin da kuma goge tarihin wayewar 'yan nahiyar tun kafin zuwan Turawa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng