Forbes: Adenuga Ya Doke BUA, Ya Dawo Bayan Dangote a Jerin Attajiran Najeriya
- Mike Adenuga shi ne na biyu a rukunin attajiran Najeriya kamar yada mujallar Forbes ta fitar da rahoto
- Sababbin bayanan da aka fitar a shekarar 2024 da aka shiga sun nuna an sha gaban Abdussamad Rabiu
- Baya ga harkar sadarwa, Adenuga mai shekara 72 a duniya yana harkar kasuwancin mai a duniya
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Mr. Mike Adenuga ya dawo matsayinsa a rukunin attajiran Najeriya, ya tabbata a matsayin na biyu a kasar nan.
Mujallar Forbes ta fitar da jerin masu kudi a shekarar nan ta 2024, Mike Adenuga yana gaban Alhaji Abdul Samad Rabiu.
Adenuga a #2, Abdul Samad Rabiu a #3
Shugaban kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu ya koma na uku a jerin da aka saki yanzu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Mike Adenuga mai Dala biliyan $7.4 ya yi suna da kamfanin sadarwa na Globacom wanda shi ne na uku a Najeriya.
Ya aka yi Mike Adenuga ya motsa?
Rahoto ya nuna darajar kamfanin Globacom ya taimaka wajen farfadowar Adenuga bayan ya dawo na uku a watannin baya.
Duk kasar nan, Aliko Dangote ne kurum yake gaban Adenuga, shugaban kamfanin na Dangote Group kuwa bai da sa’a a Afrika.
Yadda Adenuga ya sullubo a 2023
Nairametrics ta ce Adenuga ya sullubo ne da ya rasa fam $3.6bn daga cikin Dala biliyan $6.3 a tsakiyar shekarar 2023.
Masana sun ce rashin cinikin Conoil da karya darajar Naira ya taimaka wajen rage tarin arzikin da Adenuga ya mallaka.
A shekarar 2015, sai da ta kai Adenuga ya ba Dala biliyan $10bn baya, amma daga baya ya yi ta fuskantar wasu kalubale.
Kwanan nan an ji labari hukumar NCC ta amince a hana masu layin Globacom kiran MTN saboda kin biyan wasu bashin kudi.
Wahalhalun da Adenuga ya sha
A shekarar 2006, hukumar EFCC ta taba binciken kamfanoninsa irinsu Globacom, bankin Equitorial Trust Bank (ETB) da Conoil.
Wannan ya jawo attajirin ya tsere zuwa Landan, bai dawo Najeriya ba sai da shugaba Umaru Musa Yar’Adua ya yi masa afuwa.
Adenuga yana cikin attajiran Afrika
Kamar kowace shekara, Aliko Dangote da wasu tsirarun ‘yan Afrika su na cikin Attajiran Duniya, haka abin yake a 2024.
Ana da labari a lissafin Forbes, AbdulSamad Rabiu, Mike Adenuga da Nassef Sawris sun ba kusan Naira tiriliyan 15 baya yanzu
Asali: Legit.ng