Rupert: Labarin Attajirin da Ya Gwabje Dangote a Matsayin Mai Kudin Afrika a 2024
- Johann Rupert wanda shi ne shugaban kamfanin Compagnie Financiere Richemont ya fi kowa kudi a Afrika
- Mai kudin da ya zarce Alhaji Aliko Dangote a shekarar nan ta 2024, yana da hannun jari a kamfanin Remgro
- Asalinsa mutumin kasar Afrika ta Kudu ne kuma mahaifinsa babban ‘dan kasuwa ne wanda ya tashi a Graaff-Reinet
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
South Africa - Johann Rupert shi ne shugaban kamfanin Compagnie Financiere Richemont wanda ya yi suna da Cartier da Montblanc.
An haifi Johann Ruppert ne a shekarar 1950 yanzu haka yana rayuwa a birnin Cape Town, ana hasashen arzikinsa ya kai $10.3bn.
Kafin ya kai wannan matsayi, Aliko Dangote ya yi shekaru kimanin 12 a matsayin na daya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mecece silar arzikin Johann Rupert?
Attajirin mai ‘ya ‘ya uku a duniya ya yi arziki ne ta hanyar kayan kwalisa kuma ya mallaki kungiyar wasan Rugby a kasar Birtaniya.
Mahaifinsa Anton ya fara kafa kamfanin Rembrandt Group Limited a shekarun 1940s wanda a yanzu aka fi sani da Remgra Ltd.
Baya ga hannun jarin 7% a Remgra, Forbes ta ce Johann Rupert yana cikin masu kamfanin Reinet da ke kasar Luxembourg.
Richemont ta ce a shekarar 2010, kamfaninsa ya saye Net-a-Porter a kan fiye da $500m yanzu a duk kasashen Afrika bai da tamka.
Ilmi da karatun Johann Rupert
Bayan ya kammala karatun ilmin tattalin arziki da dokokin kamfanoni a jami’ar Stellenbosch, ya fara aiki a kamfanin mahaifinsa.
Yanzu yana da digirin karramawa a bangarorin shari’a, tattalin arziki da kuma kasuwanci da lambar girman Legion d'Honneur a kasar Faransa.
Yaushe Rupert ya fara neman kudi?
Kafin ya kafa Richemont, bayanai sun nuna attajirin ya bude wani banki mai suna Rand Merchant Bank shekaru 45 da suka wuce a Afrika.
Kafin nan ya yi aiki a bankin Chase Manhattan Bank da Lazard Frères a birnin New York.
Tun 2007 ya shiga yarjejeniya da Polo Ralph Lauren, ya mallaki 50% na kamfanin. Har yau yana mai nadamar rashin sayen kamfanin Gucci.
Johann Rupert ya yi ritaya
Duk da ya yi ritaya daga manyan ayyuka, har yau shi ne shugaban gidauniyar Peace Parks Foundation da gidauniyar Michelangelo Foundation.
Da ya tafi hutu a 2013 sai ya nada Yves-Andre Istel ya zama sabon shugaban kamfaninsa.
Su wanene Attajiran Afrika?
Rahoto ya zo dauke da sunayen masu kudin nahiyar Afrika:
1. Johann Rupert: $10.3bn
2. Aliko Dangote: $9.5bn
3. Nicky Oppenheimer & Family: $8.3bn
4. Nassef Sawris: $7.4bn
5. Abdul Samad Rabiu: $5.9bn
6. Nathan Kirsh: $5.8bn
Kamfanin Allura da Sirinji mafi a girma a Afirka ya rufe ofishinsa na Najeriya, ya faɗi dalili 1 tak
7. Issad Rebrab and Family: $.6bn
8. Mohammed Mansour: $3.6bn
9. Naguib Sawris: $3.3bn
10. Mike Adenuga: $3.1bn
Asali: Legit.ng