Jerin Biloniyoyin Afrika 10: Dangote, Rabiu da Adenuga Sun Bayyana a Sama

Jerin Biloniyoyin Afrika 10: Dangote, Rabiu da Adenuga Sun Bayyana a Sama

  • Biloniyoyin 19 na nahiyar Afirka daga kasashe bakwai wadanda jimillar dukiyarsu ta kai $18 biliyan sun zama sha kallo
  • 'Yan Najeriya guda uku sun shiga jadawalin jerin goma na farko a kididdigar da Forbes ta yi na biloniyoyin Afirka
  • Sama da shekaru 12, Dangote ya tsaya a matsayinsa na farko, yayin da Johann Rupert na Afirka ta kudu ya tsaya a na mataki na biyu

Kamar yadda mujallar Forbes ta bayyana biloniyoyin Afirka sun tafka asarar jimillar $3.1 biliyan a watanni 12 da suka shude.

Masu Kudi
Jerin Biloniyoyin Afrika 10, 3 na Farko Duk 'Yan Najeriya ne. Hoto daga Bloomberg / Contributor
Asali: Getty Images

Biloniyoyin Afirka guda 19 jimillar dukiyarsu ta kai kimanin $18.5 biliyan, wanda ya yi kasa da $84.9 biliyan a 2021, duk da samun sabbin biloniyoyi a jerin.

Saukar kashi 4 ya biyo bayan karin kashi 15 na farashin kayayyaki a fadin Afirka.

Kara karanta wannan

Tinubu Gida-gida: Yadda Aka Gudanar Gangamin Tallata Tinubu Da Shettima Har Gida Ga Mazauna Wata Jahar Arewa

Biloniyoyi daga kasashe bakwai cikin kasashe 54 sun shiga jerin sunayen Forbes. 'Yan Najeriya uku sun shiga jadawalin jerin sunayen Forbes, Aliko Dangote, 'dan Najeriyan da ya fi kowa arziki da dabarbarun sarrafa abubuwa, wanda ya tafka asarar $400 miliyan ya hango dukiyarsa $114.5 biliyan tsaye da kafafunta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dangote yana nan a matsayin mutumin da yafi kowa kudi a Afirka tsawon shekaru 13 a jerin inda hamshakin 'dan kasuwar Afirka ta kudu, Johann Rupert a matsayin na biyu da kimanin $10.7 biliyan a matsayin jimillar dukiyarsa.

'Yan Najeriyan da suka shiga jerin sunayen a halin yanzu sun hada da shugaban kamfanin BUA, Abdulsamad Rabiu a matsayin na hudu a jerin da jimillar dukiya $7.6 biliyan.

Yayin da mai kamfanin Globacom, Mike Adenuga ya tsaya a na 6 da jimillar dukiya $6.3 biliyan.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Tsohon Gwamnan Fitacciyar Jihar Arewacin Najeriya Ya Riga mu Gidan Gaskiya

Rahoton da Forbes ta yi ya bambamta da kididdigar Bloomberg Billionaire inda Dangote ya sauka zuwa matsayi na 84 daga na 80 da ya tsaya a watan Janairu gami da tafka asarar kimanin $8 miliyan.

A jerin sunayen Blomberg, Dangote na da jimillar kimanin $19 biliyan, inda aka saka shi a matsayin mai samar da kayayyaki.

Manyan Biloniyoyin da ke jerin sunayen Forbes sune;

1. Aliko Dangote: $13.5 biliyan

2. Johann da iyalai: $10.7 biliyan

3. Nicky Oppenheimer da Iyalai: $8.4 biliyan

4. Abdulsamad Rabiu: $7.6 biliyan

5. Nassef Sawiris: $7.3 biliyan

6. Mike Adenuga: $6.3 biliyan

7.Issad Rebrab da Iyalai: $4.6 biliyan

8. Naguib Sawiris: $3.3 biliyan

9. Patrice Motsepe: $3.2 biliyan

10. Muhammad Mansour: $2.9 biliyan

Manyan masu arzikin duniya sun tafka asara, Dangote ya samu karuwa

A wani labari na daban, ranar Litinin da ta gabata ta kasance bakar rana ga wasu hamshakan masu arzikin duniya saboda asarar da suka tafka.

Billgates, Elon Musk, Jeff Bezos da wasu biloniyoyin duniya sun tafka asara amma Alhaji Aliko Dangote ya samu karuwar arziki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel