“Da Gaske Yana Aiki”: Mutumin Bayelsa Ya Gwada Baiwarsa, Ya Kera Keke Mai Tafiya Akan Ruwa

“Da Gaske Yana Aiki”: Mutumin Bayelsa Ya Gwada Baiwarsa, Ya Kera Keke Mai Tafiya Akan Ruwa

  • An saba ganin ana tuka kekuna a kasa, amma wani mai kirkira ya samar da wanda za a iya amfani da shi a cikin ruwa
  • Mutumin wanda dan asalin jihar Bayelsa ne, ya kera keken ruwa ne kuma gwada shi ta hanyar tuka shi a kan Kogi
  • Hotunan wannan mutumi mai hazaka da ke amfani da fasaharsa ya baiwa masu amfani da yanar gizo mamaki, inda da dama ke yaba masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Bayelsa - Wani dan Najeriya mai suna Tari Ibruku ya kera keken zirga-zirga akan hanyoyin ruwa.

Shafin NigerDelta Insider, da ya ruwaito labarin mutumin, ya ce Tari ya fito daga Twon-Brass a Kudancin Bayelsa kuma yana jin dadi idan aka kira shi da "Mu je zuwa."

Kara karanta wannan

Mummunan hatsari ya lakume rayukan akalla mutum 6 a babban titin Kaduna zuwa Zariya

Mutumin Bayelsa ya kera keke mai tafiya kan ruwa
Tari Ibruku ya ce sai da ya shafe wata hudu kafin ya kera keken ruwan. Hoto: NigerDelta Insider
Asali: Facebook

Watanni hudu aka yi ana kera keken ruwan

A cewar shafin na Facebook, Tari ya gwada keken ruwansa a wani kogi kwanakin baya kuma ya tabbatar da cewa yana aiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tari ya ce ya kwashe watanni hudu yana kera keken. Hotunan da NigerDelta Insider ya wallafa sun nuna Tari yana amfani da keken ruwa akan kogi.

Masu amfani da yanar gizo sun yabi Tari, yayin da suka kara masa kwarin guiwa, yayin da kuma wasu suka nuna sha'awar son mallakar keken da ya kera.

Jama'a na yabawa Tari Ibruku

Amakson Fab ya ce:

"Ina tayaka murna dan uwa, ka ci gaba da aikin ka."

Engr Onyebuchi Okafor ya ce:

"Wannan babbar fasaha ce, ka ci gaba da yin aiki tukuru."

Pst Henry Ebitimi ya ce:

"Ina son in mallaki daya nan ba da jimawa ba, na taya shi murna."

Kara karanta wannan

"Ka nemi mata": Maratanin jama'a yayin da Dino Melaye ya koka da rayuwar kadaici, bidiyon ya yadu

Kakkyawar fasaha: Dan shekara 20 a Arewacin Najeriya ya kera jirgin sama

A wani labarin na daban, wani matashi dan shekara 20 mai suna Yahaya Usman Ahmad ya kera wani jirgin sama, kuma ya kammala karatun digirin sa na farko a lokacin.

Matashin dai ana hasashen ya fito daga garin Yola, jihar Adamawa, wanda wani Malik Ibrahim ya fara dora hotunan jirgin da Yahaya ya kera a shafuka sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel