Yaro-mai-fasaha: Wani dan shekara 20 a Arewa ya kera kayataccen jirgin sam (Hotuna)
Hakika matasan Najeriya musamman ma na yankin arewacin kasar Allah ya albarkace su da dumbin fasaha da basira da masu fashin baki kan harkokin yau da kullum ke ganin taimako kawai suke bukata domin su yi zarra a duniya baki daya.
A kasashe da dama dai akan samu 'yan Arewacin kasar da kan je su kuma nuna bajintar su har ma a wasu wuraren su yi zarra a fannonin da suka dauka kamar dai yadda muka sha gani a kasashe da dama.
KU KARANTA: Atiku ya fadi fannin da gwamnatin Buhari tafi kwarewa
Legit.ng Hausa yanzu ma tana dauke ne da labarin wani matashin da duka-duka ke da shekaru 20 a duniya daga yankin arewacin Najeriya da ya kera wani butum-butumin jirgin sama da wasu karafa da ya tattaro.
Matashin mai suna Yahya Usman Ahmad wanda muka samu labarin cewa ya kammala karatun sa na digirin farko fannin lissafi a Kwalejin koyon malunta dake garin Yola babban birnin jihar Adamawa ance ya fita ne da daraja ta farko.
Labarin matashin dai wani bawan Allah ne mai suna Malik Ibrahim Jalo Jalingo ya fara yada shi a kafafen sadarwar zamani kafin daga bisani wakilin mu ya yi bincike kan sa.
Ga karin hotunan sa nan:
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng