Masu amfani da yanar gizo a Najeriya sun kai miliyan 113.8 - NCC
An bayyana adadin masu amfani da yanar gizo a Najeriya sun kai miliyan dari da goma sha uku da dubu dari takwas, (113,800,000) zuwa watan Janairu, kamar yadda hukumar sadarwa ta Najeriya, NCC, ta ruwaito.
NCC ta bayyana haka ne a ranar Juma’a, 1 ga watan Maris, a yayin da suke bayanin jawaban ayyukansu na wata wata, inda suka ce adadin masu amfanin da yanar gizo a Najeriya a watan Janairu sun kai 113,875,204.
KU KARANTA: Nasarar cin zabe: Kungiyar kasashen nahiyar Afirka gaba daya ta taya Buhari murna
Hakan ya nuna adadin jama’an ya karu da miliyan biyu da dubu dari biyu da arba’in da biyu da sittin da tamanin da takwas (2,242,688), daga watan Disambar bara inda adadin masu amfani da yanar yake a miliyan 11,632,516 (111,632,516).
Hukumar NCC ta bayyana cewa kamfanin sadarwa na Airtel da MTN ne suka fi samun karin masu amfani dasi, yayin da kamfanin 9mobile da Globacom sune suka fi tafka asara a harkar ciniki da hada hada a bangaren sadarwa.
A watan janairu kadai MTN ta samu karin ma’abota hulda da suka kai miliyan biyu da dubu talatin, (2,031,214) wanda hakan ya kawo karin adadin masu amfani da kamfanin zuwa miliyan 45.93 daga miliyan 43.89.
Yayin da kamfanin Airtel ta samu karin masu amfani da layinta daga miliyan 29.75 zuwa miliyan 30.46, daga watan Disamba zuwa watan Janairu, su kuma kamfanin Glo sun yi asarar masu abokan huldansu guda 454,409.
Hakan ya nuna abokan huldarsu sun ragu daga miliyan 28,054,948 zuwa 27,600,539. Inda kamfanin 9Mobile suka rasa mutane 36,854, wanda hakan ya nuna ma’abota aikin kamfanin sun sauko daga miliyan 9.88 zuwa 9.91.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng