Soyayya ruwan zuma: Budurwa ta tara N1.8m, ta bawa saurayinta kyauta domin ya sayi mota
- Budurwa ta tara kudi masu tarin yawa domin ta bawa saurayinta ya sayi mota
- Budurwar ta ce saurayin nata ya cancanci haka, domin tunda take dashi ba ta taba kama shi da wata ba
- Ta ce shima yana tara kudin, amma ita bata sanar da shi cewa tana tara nata ba har sai da yazo sayen motar
Wata budurwa mai suna Koko ta bayyana yadda ta tara wasu makudan da niyyar ta bawa saurayinta ya sayi motar da zai dinga hawa yana kece raini shi ma.
Koko ta bayyana cewa ta tara har dala dubu biyar ($5000), kimanin naira miliyan daya da dubu dari takwas kenan (N1.8m), kuma duka tayi hakane domin ta bawa saurayin nata ya sayi mota.
Ta ce saurayin nata bai san cewa tana tara kudin ba, shima lokacin yana tara nashi, a karshe suka tara dala dubu goma ($10,000), kimanin naira miliyan 3 da dubu dari shida kenan (N3.6m).
KU KARANTA: An fi kama turawa da laifin ta'addanci fiye da sauran mutane na duniya - Bincike
Da ta wallafa a shafinta na Twitter, Koko ta ce: "Saurayina yana tara kudi kowanne wata har ya tara dala dubu biyar domin ya sayi sabuwar mota gobe.
"Abinda bai sani ba shine, yana da dala dubu goma ne. Nima ina tara kudin a boye bai sani ba, ya cancanci haka sosai. "Muna tare tsawon shekara 6, ban taba zuwa na same shi da wata mace ba. Bamu haihu ba, amma yana biyan kudin gida ni kuma ina biyan na kayan abinci."
Alamu na nuni da cewa yanzu an dawo lokaci da 'yammata ke siyawa samari motoci, domin kuwa a kwanakin baya mun kawo muku labarin wata budurwa 'yar asalin garin Fatakwal da ta tara kudi masu tarin yawa ta siyawa saurayinta sabuwar mota kirar Toyota Corolla.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng