Zo Ka Nemi Aiki: Dan Najeriya Ya Nemo Kamfanin da Ke Biyan Albashin Naira Miliyan 3 Duk Wata
- Dan Najeriya ya fadi wasu ayyuka guda biyu da mutum zai iya nema wanda ke biyan naira miliyan uku duk wata
- Kamfanonin dai na aiki ne a Abuja kuma suna neman kwararre da zai kama aiki a guraben da zai samu kudade masu yawa
- Mutane da yawa sun karyata bayaninsa, sai dai jim kadan bayan da ya tura adireshin kamfanonin, an tabbatar da ikirarinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Wani dan Najeriya ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa akwai guraben aiki da za a biya albashin naira miliyan uku duk wata.
Mutumin mai amfani da sunan @3mbeeeee a Twitter ya bayyana cewa a Abuja ake yin aikin kuma kamfanonij na neman kwararru da za su kama aiki nan take.
Sai dai da yawa ba su gamsu da wannan bayanin na sa ba, inda daga bisani ya wallafa adireshin neman aikin don tabbatarwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Legit ta tattaro cewa kamfanin na neman kwararru a fannin 'warware rikici' da kuma 'mawallafi kan kyawun halittu'
Ana iya samun karin bayanai kan ayyukan anan da nan.
Duba wallafarsa a kasa:
Ma'aikatan tarayya 2,000 sun rasa albashin watan Nuwamba
A wani labarin, kun karanta cewa akalla ma'aikatan gwamnatin tarayya dubu biyu ne suka rasa albashin su na watan Nuwamba, kamar yadda majiya mai tushe ta bayyana hakan a ranar Litinin.
Wani ma'aikaci gwamnati a ma'aikatar tsaro ta kasa, ya yi nuni da cewa da yawa daga cikin ma'aikatan da ke aiki a ma'aikatar ba su samu albashin su ba, Legit Hausa ta ruwaito.
Ma'aikacin gwamnatin ya kuma yi nuni da cewa gaza samun albashin ba zai rasa nasaba da tantancewa da ofishin shugaban ma'aikatan tarayya da ke yi a kasar ba.
Da gaske gwamnati ta yi gwanjon babban otel mallakin jihar Kwara?
A wani labarin na daban, a yayin da ake ci gaba da yada jita-jitar cewa an cefanar da babban otel mallakin jihar Kwara, gwamnatin jihar ta fito ta yi martani akai.
Gwamnatin jihar ta ce babu wani dalili da zai saka a sayar da otel din, kawai ta yi gwanjon kayan cikinsa ne don yin gyare-gyare.
Asali: Legit.ng