"Ba Ya Yi Min Magana": Budurwar da Ta Ba Saurayinta Kyautar Sabbin Kaya Ta Nemi Ya Biya N10k Ta Koka

"Ba Ya Yi Min Magana": Budurwar da Ta Ba Saurayinta Kyautar Sabbin Kaya Ta Nemi Ya Biya N10k Ta Koka

  • Wata budurwa ƴar Najeriya ta shiga damuwa bayan saurayinta ya fusata ya daina magana da ita
  • A cewarta, masoyin nata ya fusata ne saboda ta buƙaci ya kammala biyan kuɗin wani kayan da ta ɗinka masa
  • Masu amfani da shafukan sada zumunta sun bayyana ra'ayoyinsu game da lamarin tare da sukar matakin da budurwar ta ɗauka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Wata ƴar Najeriya ta bayyana abin da ya faru a baya-bayan nan tsakaninta da saurayinta wanda a halin yanzu yake rikici da ita.

Budurwar mai amfani da sunan @Benita a Twitter ta ba da labarin yadda ta yanke shawarar ɗinka wa saurayin nata sabbin kaya bayan ta lura yana buƙatar sabbi.

Kara karanta wannan

"Ina son mahaifinsa idan yana raye don Allah": Matashiya ta fadi dalilinta na auren tsoho

Budurwa ta koka kan saurayinta
Budurwar ta ce saurayinta ya daina mata magana Hoto: @beninitq/TikTok, @mixetto/Getty Images (hoton an yi amfani da shi ne kawai domin misali)
Asali: UGC

Budurwar ta jawo cece-kuce bayan da ta nemi saurayi ya biyan kuɗin kaya

A cewarta, ta tuntubi wani tela domin ya yi wa masoyinta tufafin kuma kudin kayan ya kai N15,000.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta biya N5k sannan ta nemi saurayin nata ya kammala biyan kuɗin ta hanyar ƙara N10,000.

Sai dai saurayin nata ya fusata ya daina yi mata magana don ta ce masa ya cika ragowar kuɗin kayan.

A kalamanta:

"Na lura saurayina na bukatar sabbin tufafin sanya wa, don haka na yanke shawarar na tuntuɓi wani tela don ya ɗinka masa wasu ba tare da saninsa ba, na gabatar masa da su a safiyar yau, na ce masa kyauta ce da na ba shi."
"Jimillar kuɗin kayan 15k na biya 5k saura 10k na neme shi ya taimaka ya kammala biyan kuɗin sai ya fusata ya ƙi yi min magana me nayi?"

Kara karanta wannan

Gwamna Lawal ya sake tono zunzurutun bashin da tsoffin gwamnoni biyu suka bar masa tun daga 2015

Wane martani ƴan soshiyal midiya suka yi?

Rubutun ya jawo martani da yawa daga masu amfani da yanar gizo waɗanda suka caccake ta kan neman kuɗi daga saurayin nata.

@Akachukwuu_you ya rubuta:

"Kin yi wa saurayinki kyauta kuma kina son ya biya kuɗin kyautar? Lmao."

@Neriahs_world ya rubuta:

"Sai ya biya kuɗin abin da bai sanya ki ba?"

@Imperialpresh ya kara da cewa:

"Baku son ku kashe kudi akan wasu amma kuna so idan sun kashe muku kuɗi."

@bgl_tweets ya rubuta:

"Wannan ba kyauta bane aunty, kina son cinye masa kuɗi ne."

@Godsplan009 ya rubuta:

"Me yasa tun farko baki gaya masa ba."

Budurwa Ta Kamu da Son Ɗan Ajinsu

A wani labarin kuma, wata budurwa ta kamu da son ɗan ajinsu lokacin da suke karatu a makaranta, inda daga ƙarshe suka zama miji da mata.

Budurwar mai suna, Nortie Ehlla, ta sanya wani bidiyo akan TikTok domin yi wa mabiyanta ƙarin bayani, bayan an sha shagalin bikinsu ita da mijinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel