'Ka Yi Sha'anin Gabanka': Mai Gida Ya Gargadi Mai Haya Da Ya Bar Kula Matarsa Ko Ya Fuskanci Kora

'Ka Yi Sha'anin Gabanka': Mai Gida Ya Gargadi Mai Haya Da Ya Bar Kula Matarsa Ko Ya Fuskanci Kora

  • Wani mai gidan haya ya gindaya wa matashi mai haya a gidansa sharuda tsaurara kan gaisuwa da suke yi da matarsa
  • Mai gidan ya ce ya kula yana yawan gaisawa da matarsa shi kuma ya tsani hakan, ya masa barazanar kora a gidan
  • Mai hayan a nashi bangaren ya ce yana jin dadin zama a gidan gashi akwai wutar lantarki wadatacce a gidan

Wani dan haya ya sha mamaki yayin mai gidan haya ya gindaya masa sharuda akan matarsa daga shigansa gidan bai ko dade ba.

A wani sakon sirri da aka wallafa a Twitter, mutumin ya ce mai gidan hayan ya ce masa kada ya kuskura ya sake gaishe da matarsa.

Mai gida gargadi mai haya akan kula matarsa, ya masa barazanar kora
Mai Gida Da Dan Haya. Hoto: Getty Images/SeventyFour, Hill Street Studios and Renata Angerami.
Asali: Getty Images

Ya ce mai gidan ya yi barazanar korarshi a gidan idan suka ci gaba da gaishe da juna.

Kara karanta wannan

'Rashin Da'a Ga Buhari': Tajudeen Abbas Ya Barranta Kansa Da Kalaman Hadiminsa

Mai hayar ya fadi irin gargadin da aka masa akan gaisuwa

Mai hayar ya ce yana jin dadin gidan saboda akwai wutar lantarki kuma yana kusa da gari, Legit.ng ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma ya ce ya yi mamakin yadda abubuwa suka koma, ya rubuta cewa:

"Ina aiki daga gida, na shiga wannan gida wanda yake da wutar lantarki kullum ga tsafta ga shi kusa da gari.
"Makon da ya gabata na dawo daga majami'a muna gaisawa da matar mai gidan, kawai sai mai gidan ya ce ko na bar kula matarsa ko kuma ya kore ni a gidan."

Wizarab shi ya fara wallafa labarin yayin da @instablog9ja ya kara wallafawa.

Mutane sun tofa albarkacin bakinsu:

@MmaNwosu:

"Kawai ka yi harkokinka gaisuwa ba dole ba ne, kana son fita ne?"

@_Gabri3llaa:

Kara karanta wannan

Allah Daya Gari Banban: Yadda Aka Sha Shagalin Bikin Wani Basarake Da Amaryarsa Kada

"Gayen mai kyau ne kuma matar mai gidan ta na son kyawawa."

@KayceeRad:

"Idan ba ka da wani abu tsakanin ka da ita, ban ga dalilin rashin gaishe ta zai zama matsala ba, tabbas kana son sabon gidan, don haka ka yi biyayya ka ci gaba da zama."

Matashi Kuma Makaho Da Ke Amfani Da Wayar ‘IPhone’ Ya Girgiza Intanet

A wani labarin, wani matashi makaho ya bayyana yadda ya koyi amfani da wayar IPhone.

Makahon mai suna Waziri Ahmed ya bayyana yadda makantar ta same shi lokacin da yake tuki.

Ya ce ya gamu da 'yan fashi inda suka bukaci ya basu wayar hannunsa a kokarin ba su wayar sai suka harbe shi a fuska.

Asali: Legit.ng

Online view pixel