Karatun Karshe da Sheikh Abubakar Giro Argungun Ya Yi Kafin Ya Komawa Allah
- Abubakar Giro Argungu ya gabatar da karatun tafsirin Al-Kur’ani har ana gobe zai bar duniya
- A karshen karatun, an yi sallama da nufin malamin musuluncin zai cigaba da darasi washegeri
- Malamin ya karar da lokacin rayuwarsa wajen karantar da addini da gwagwarmaya a Najeriya
Kebbi - Ana saura sa’o’i kadan ya bar Duniya, Abubakar Giro Argungun ya gudanar da darasin tafsiri watau ilmin ma’anonin Kur’ani.
Abubakar Giro Argungun ya yi karatun ne a ranar 5 ga watan Satumba 2023 wanda ya zo daidai da Talata, 21 ga watan Safar 1445.
Kamar yadda wani mai suna IZALA ya wallafa bidiyo a shafinsa na X watau Twitter, a karshen karatun ne ya amsa tambayoyin jama’a.
Falalar zikiri bayan sallah - Gero
Malamin ya yi magana a kan muhimmancin zikirori da ake yi bayan sallolin farilla a musulunci, ba da dadewa ba sai aka ji labari ya cika.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘La ilaha illal Lah wahdahu la sharika Lahu, Lahul Mulku wa lahul hamd, wa huwa ala kullu shai’in Qadir'
Marigayi Giro Argungu ya ambato hadisi a game da falalar addu’ar da ake yi a ranar Arafah, ya ce hakan ya zo a littatafan hajji da umrah.
A cewar malamin addini, babu addu’ar da Ubangiji Sarki (SAW) yake so kamar wanda aka yi a lokacin tsayuwar Arafah a watan Zul Hajj.
Giro Argungu zai cigaba da karatu a gobe
Shehin yake cewa a zikirin babu inda aka ambaci bukatar duniya illa neman albarkacin Ubangiji wanda aka tsarkake tare da ba Shi girma.
An kammala karatun ne da nufin za a cigaba zuwa Laraba, a yammacin ranar ne malamin ya rasu.
Hakan ya faru bayan babban malamin ya yi fama da ciwon da ya yi sanaddiyar da ya yi doguwar jinya a asibitin kasar waje kafin ya warke.
Bidiyoyi Da Hotuna Sun Bayyana Yayin da Ganduje, Keyamo, Bala Mohammed Da Sauransu Ke Likimo a Kotun Zaben Shugaban Kasa
Afuwar Abubakar Giro Argungu
A shekarar bara aka rahoto Shiekh Abubakar Giro Argungu ya nemi afuwar 'yan Najeriya a kan wani bidiyonsa da yake yawo a Najeriya.
Fai-fan ya nuna malamin yana kakkausan kalamai kan "makiya" Shugaba Muhammadu Buhari, daga baya ya ce ba haka yake nufi ba.
Asali: Legit.ng