Mutane Sun Cika Da Mamaki Bayan Tsohuwa Ta Dawo Yarinya Saboda Kwalliyar Da Ta Sha

Mutane Sun Cika Da Mamaki Bayan Tsohuwa Ta Dawo Yarinya Saboda Kwalliyar Da Ta Sha

  • Wani bidiyon kwalliyar da aka rangaɗawa wata tsohuwa ya bar mutane baki buɗe cike da mamaki kan abinda idon su ya gane musu
  • A cikin bidiyon wanda wata mai sana'ar kwalliya @unusualglams19, ta sanya a TikTok, tsohuwar ta sauya kamanni gaba ɗaya bayan an gwangwajeta da kwalliya
  • Masu amfani da yanar gizo da dama da suka kalli bidiyon sun garzaya wajen sharhi domin bayyana ra'ayoyin su

Wani sauyi da aka samu bayan an rangaɗawa wata tsohuwa kwalliya, ya bar mutane cike da mamaki saboda yadda tsohuwar ta koma kamar wata matashiyar budurwa, bayan an gwangwaje ta kwalliya.

Kwalliya ta mayar da tsohuwa yarinya
Tsohuwa ta koma budurwa bayan ta sha kwalliya Hoto: @unusualglams19
Asali: TikTok

Wata ƴar TikTok mai yin kwalliya wacce ke amfani da sunan @unusualglams19, ta sanya mutane sun yi ta ruwan tambayoyi bayan ta sanya bidiyon tsohuwar na kafin a yi mata kwalliyar da na bayan an yi mata kwalliya.

Kara karanta wannan

"Dole Sai Yana Samun N3m": Budurwa Mai Samun N3.7m a Wata Ta Bayyana Irin Mijin Da Ta Ke Son Yin Wuff Da Shi

Abinda ya ɗauki hankulan mutane shine yadda tsohuwar ta tashi daga kamannin tsufa tukuf ta koma wata matashiyar budurwa mai jini a jika.

Ƴan soshiyal midiya sun cika da mamaki

Sauyin kamannin da tsohuwar ta samu ya sanya mutane shiga cikin matuƙar mamaki da tunanin ta ya hakan ta kasance. Hakan ya sanya aka yi ta tafka mahawara kan yadda kwalliya ta zama wani sabon salo na rage tsufa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ajosetosin1 ya rubuta:

"Kai ban yarda ba."

user1590654632196:

"Shin kin tabbata itace kuwa?"

Efemoney101 ya rubuta:

"Yakamata a haramta yin kwalliya kwata-kwata."

SpongeBob's wife ta rubuta:

"Daga shekara 89 zuwa 34."

Priscilla Asante ta rubuta:

"Kai wannan ta sha gyara sosai."

omo ya rubuta:

"Kai ya zama dole a ji tsoron masu yin kwalliya."

Temmy Trendz:

"Shiga aljannah zai yi wa masu ƙwalliya wahala, saboda menene wannan."

Kara karanta wannan

Bidiyon Wata Budurwa Da Ta Durfafi Coci Da Nufin Samo Miji Ko Ta Wane Irin Hali

Matashi Ya Fusata Bayan Wacce Zai Aura Ta Nemi Ya Kawo N12m

A wani labarin na daban kuma, wani matashi mai shirin angwancewa da wacce zai aura, ya fusata bayan an nemi ya kawo kuɗin da za a shirya bikin aurensu, waɗanda yawansu ya kai N12m.

Matashin ya ce sam ba za ayi wannan shiriritar da shi ba, inda ya ce ya fasa yin auren gaba ɗaya tunda haka abin ya koma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel