Gwarzon Maza: Matashi Ya Auri Mata Biyu a Tare, Sun Samu Juna Biyu Lokaci Daya

Gwarzon Maza: Matashi Ya Auri Mata Biyu a Tare, Sun Samu Juna Biyu Lokaci Daya

  • Wani matashi mijin wasu matasa mata guda biyu ya bayyana cewa dukkanin su sun haihu a lokaci ɗaya
  • Matashin ya bayyana cewa matan nasa a lokaci ɗaya suka samu juna biyu suka haifi wanda ya sanyawa sunan Pendo da Favian.
  • Ya sanya wani bidiyo a TikTok domin murnar wannan baiwa da ya samu, amma mutane sun yi bayyama mabambantan ra'ayoyi
  • Wani matashi ya yaɗu a manhajar TikTok bayan ya sanya bidiyon kyawawan matan sa guda biyu.

A wani bidiyo da ya sanya a shafin sa na TikTok mai suna, @wamaiyu, matashin ya bayyana cewa matan sa lokaci ɗaya suka samu juna biyu.

Matan aure
Gwarzon Maza: Matashi Ya Auri Mata Biyu a Tare, Sun Samu Juna Biyu Lokaci Daya Hoto: TikTok/@wamaiyu
Asali: TikTok

Bayan kuma samun baiwar ɗaukar juna biyun su a tare, matashin ya kuma bayyana cewa matan nasa lokaci ɗaya suka haihu.

A cikin bidiyon, an nuna matan nasa ɗauke da rusheshen junan biyun yayin da ake ɗaukar su hoto suna cikin farin ciki.

Kara karanta wannan

"Ki Bar Bawan Allah Ya Huta": Bidiyon Wata Budurwa Da Saurayinta Suna Jin Daɗi a Dakin 'Hotel' Ya Girgiza Mutane

Sai dai matashin bai nuna hotunan jariran da aka haifa masa ba, amma ya gayawa masu bibiyar sa cewa ya raɗa musu suna Pendo da Favian.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutane sun yi sharhi sosai a kai

Mutane da dama sun bayyana mabanbanta ra'ayoyi akan bidiyon. A yayin da wasu suka yaba musu saboda haɗin kan su, wasu kuwa cewa suka yo ba zasu iya rayuwa da kishiya ba.

Ga kaɗan daga ciki:

@Chepngasuret ya rubuta:

"Wannan shine abinda ake kira da so. Yafi ace kana da mata biyu da ace kana cin amanar matar ka a waje. Ka burgeni ɗan'uwa ina tayaka murna."

@Nancy ta rubuta:

"Ina tunanin ƴan ƙasar Uganda ne."

@cesswab ya rubuta:

"Yanzu da suke can suna jinya, kana buƙatar ta uku."

@Linah Saisi ta rubuta:

"Ba zan iya yarda da hakan ba. Hakan zai ɓata min rayuwa ne, gwara na tsaya ban yi aure har sai lokacin da Allah ya so."

Kara karanta wannan

"Ba Wayau": Kyakkyawar Budurwa Ta Damfari Wani Matashi Da Ya Ce Yana Sonta, Ta Bar Shi Da Cizon Yatsa

N30,000 Kacal Muka Kashe: Sabbin Ma'aurata Sun Bayyana Auren Tattalin Da Sukayi

A wani labarin na daban kuma, wasu sabbin ma'aurata sun bayyana yadda suka gudanar da auren su ba tare da sun ƙure kan su ba.

Sabbin ma'auratan dai basu tsawwala ba wajen kashe kuɗi a bikin auren na su, inda suka yi tattali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel