Kyakkyawar Budurwa Tayi Watsi Da Soyayyar Wani Matashi Saboda Shekarun Sa

Kyakkyawar Budurwa Tayi Watsi Da Soyayyar Wani Matashi Saboda Shekarun Sa

  • Wata kyakkyawar budurwa tayi watsi da tayin soyayyar da wani saurayi ɗan Najeriya yayi mata bayan ta gano shekarun sa
  • A cikin hirar da suke yi, saurayin ya bayyana mata shekarun sa sannan ya tambaye ta irin abubuwan da take so kafin kwatsam ta dakatar da shi
  • Budurwar dai tace soyayaya a tsakanin su ba mai yiwuwa ba ce, inda ta gaya masa cewa ta girme shi, amma duk da haka bai haƙura ba

Wata budurwa mai shekara 30 a duniya, ta koka a shafin Twitter kan halayyar samarin Najeriya, yayin da ta sanya hirar ta da wani saurayi wanda ya nuna yana son ta.

Budurwar mai amfani da sunan @CaviarPurple a Twitter, suna cikin hira ne da saurayin lokacin da ya gaya mata cewa shekarar sa 28 a duniya sannan ya tambayeta abubuwan da take son yi.

Kara karanta wannan

Ali Ya Ga Ali: Bidiyon Yadda Budurwa Ta Yi Kicibis Da Iyayenta a “Go Slow” Tana Gaggawa Ta Koma Gida Don Ta Yi Dare a Waje

Budurwa
Kyakkyawar Budurwa Tayi Watsi Da Soyayyar Wani Matashi Saboda Shekarun Sa Hoto: Kevin Dodge, Twitter/Caviar Purple
Asali: UGC

Sai dai budurwar tayi hanzarin dakatar da shi, inda ta gaya masa cewa ta girme shi saboda haka soyayyar su ba mai yiwuwa bace.

Guiwoyin saurayin basu sare ba, inda ya bata amsa da cewa shekara 28 ɗin ya rubuta mata kuskuren rubutu ya samu amma ainihin shekarun 32 a duniya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Samari da dama sun goyi bayan abinda saurayin yayi, wanda hakan ya ɗaurewa budurwar kai.

Ga kaɗan daga ciki:

@shurley_bankz ya rubuta:

"Bari na gaya miki gaskiyar abinda ya faru. Yasan cewa shekarun sa sun fi na ki yawa amma baya son ki ga kamar yayi miki tsufa sai ya rage shekarun zuwa 28 ba tare da yasan cewa kin wuce hakan ba."
"Ɗora alhakin hakan akan kuskuren rubutu shine hanya mafi sauƙi da zai bi, eh tabbas kuskuren rubutu ne."

Kara karanta wannan

Yadda Hankalin Wata Mata Ya Tashi Gamida Dugunzuma Saboda Kama Diyarta da Wani a Otel.

@chibuzoi410 ya rubuta:

"Budurwata ta girme ni amma muna soyayyar mu ba tare da wata matsala ba. Manta da wannan soki burutsun kawai ka san inda ka nufa."

@kayzywizzzy said:

"Na ji daɗin yadda maza ke goyon bayan junan su a wajen nan."

Wata Budurwa Ta Rabu Da Saurayinta Bayan Ta Gano Sunan Sa Na Ainihi

A wani labarin na daban kuma, wata budurwa ta rabu da saurayin ta bayan ta gano sunan sa na gaskiya.

Budurwar ta fahimci saurayin nata ƙarya ya sharara mata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel