"Na Dena Soyayya": Wata Ta Koka Yayin Da Masoyinta Na Intanet Ya Ziyarce Ta A Karon Farko, Hirarsu Ya Bayyana

"Na Dena Soyayya": Wata Ta Koka Yayin Da Masoyinta Na Intanet Ya Ziyarce Ta A Karon Farko, Hirarsu Ya Bayyana

  • Wata budurwa yar Najeriya ta koka bayan ta bai wa saurayinta na soshiyal midiya izinin ya ziyarce ta a gida
  • Ran budurwar ya baci sosai bayan mutumin ya iso gidanta a birkice kuma da alamu ba mai hannu da shuni bane, ya kuma ba ta kyautan agogon roba
  • A wani hirar WhatsApp tsakanin budurwar da kawarta da ya fito, ta koka matuka ta kuma ce ta yi nadamar gayyatar saurayin gidanta

Wata budurwa wacce ranta ya baci sosai ta bayyana yadda haduwarta da saurayinta na soshiyal midiya ya karya mata zuciya.

A cewar ta, ta yanke shawarar ba za ta tafi hutu gida ba saboda saurayin na ta na intanet ya ce zai zo ya kawo mata ziyara.

Hira tsakanin budurwa da saurayi
Hira kan budurwa da ta gayyaci saurayi zuwa gidanta. Hoto: @success3535
Asali: TikTok

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Aure Mahaifin Tsohon Saurayinta Bayan Rabuwa da Shi

Amma, ta ce ta yi nadamar haduwarsu bayan ta gano matashin ba mai hannu da shuni bane kamar yadda ta yi tunani.

Ta koka cewa matashin ya siyo mata agogon roba ba tare da jaka ba.

Da ta ke bada labarin a Twitter, @success3535 ta rubuta:

"Kawata ta yanke shawarar ba za ta tafi hutu ba saboda saurayinta da suka hadu a soshiyal midiya zai kawo mata ziyara ya ganta kuma ga abin da ya faru."

Masu amfani da dandalin sada zumunta sun yi tsokaci

@vibes_N ya ce:

"Ya kamata ke da kawarki na bukatar wanda zai siya muku jaka, golden morn, corn flakes... Abin da kanwa ta za ta iya siya wa kanta. Ke da kawar ki ba ku da wani aji..."

@oxcollins ya ce:

"Kuna sa soyayya ya zama abin dariya a kwana biyun nan? Wanene ya saka wannan ka'idar, suna bawa kudi muhimmanci tun ranar farko.
"Da kin samu lokaci ki mayar da hankali a kansa, irin halin sa, babban kyautansa gare shi."

Kara karanta wannan

Ali Ya Ga Ali: Bidiyon Yadda Budurwa Ta Yi Kicibis Da Iyayenta a “Go Slow” Tana Gaggawa Ta Koma Gida Don Ta Yi Dare a Waje

@wumingift_ ya rubuta:

"Shin wadannan kasuwancin namiji suke yi. Tabbas ba shi kadai ta ke harka da shi ba. Idan tana neman karin jakuna, sai ta samu wasu karin mazan ..."

@aimthamachine_ ya ce:

"Kina bukatar wani ya siya miki jaka, golden morn da corn flakes? ba ki bukatar soyayya, kina bukatar aiki inda za ki yi awa 14 daga Litinin zuwa Lahadi."

@lawson_damiete ya yi martani:

"Ya siya jaka idan zai zo ganin ta? Ku ne dalilin da yasa maza ke yi wa mata magana duk yadda suke so. Saboda duk mayar da kanku abin siya."

Ga sakon a kasa:

Ki daina kira na masoyi: Saurayi ya yi raba jiha da budurwa kwana daya bayan haduwa, ya bayyana dalili

Wani saurayi dan Najeriya mai suna Josh ya rabu da budurwarsa, Vivian, saboda ta gaza dafa masa abinci mai dadi.

A cewar wata hirar Whatsapp da wani @JNRdeyforyou ya saka a Twitter, Vivian ta ziyarci Josh a gidansa ne kuma ta yanke shawarar yi masa girki.

Kara karanta wannan

“Muna Alfahari Da Ke”: Bidiyon Karamar Yarinya Tana Tuka Tuwo a Kan Murhu Kamar Babba Ya Girgiza Intanet

Asali: Legit.ng

Online view pixel