Amarya Ta Fusata Bayan Gano Wata Cin Amana Da Ƙawarta Tayi Da Angonta

Amarya Ta Fusata Bayan Gano Wata Cin Amana Da Ƙawarta Tayi Da Angonta

  • An samu hatsaniya a bakin titi bayan wata amarya ta fusata a dalilin gano wata gaskiya da tayi
  • Amaryar ta gano cewa babbar ƙawarta taci amanarta inda tayi lalata da angonta ana gobe a ɗaura musu aure
  • Mutane sun yi ta ƙoƙarin riƙe amaryar wacce ke cigaba da magana a fusace inda tayi barazanar fasa auren

Wata sabuwar amarya ta sharɓi kuka a gaban jama' bayan ta gano cewa angonta ya kwanta da babbar ƙawarta ana gobe a ɗaura musu aure.

Lamarin wanda ya auku a bainar jama'a ya janyo kace-nace inda mutane da dama suka taru a gaban tawagar ƴan ɗaurin auren.

Amarya
Amarya Ta Fusata Bayan Gano Wata Cin Amana Da Ƙawarta Tayi Da Angonta
Asali: UGC

A bidiyon wanda aka sanya a TikTok, mutane sun yi ƙokarin riƙe amaryar yayin da take ta yiwa wata budurwa tsawa wacce ake kyautata zaton itace babbar ƙawar ta.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Gamu da Gamonsu, An Kashe Su Baki Ɗaya Yayin da Sukai Yunkurin Kai Hari

An nuna wani matashi yana yiwa angon faɗa cikin yaren Pidgin kan cewa bai kyauta ba abinda yayi, domin yanzu ya zo ya lalata komai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amaryar a yayin da take ta faɗan nata ta bayyana cewa bata ba angon ba zata cigaba da auren ba.

An nuna budurwar da ake zargin na neman amaryar ta yafe mata wannan cin amanar da tayi mata.

Ga kaɗan daga cikin sharhin da mutane suka yi:

aishjim ta rubuta:

"Wannan abin takaici ne, na tausaya mata. Amma Allah ya kiyaye in tsaya ina faɗa akan namiji. Suna ta ɗorawa budurwar laifi, to shin angon fa.

tamah ta rubuta:

"Ba zan iya rayuwa da irin waɗannan mutanen ba, babbar ƙawa wacce zata iya ɗaukar raina saboda mijina, irin wannan mijin zai iya kwanciya da ƙanwata. Ba da ni ba, ba zan iya ba."

Kara karanta wannan

Ana Dab da Zaɓen 2023, Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Wurin Kamfe, Sun Buɗe Wuta

Miss Ri ta rubuta:

"Ai duk wanda yake riƙe ni sai na haɗa masa jini da majina. Ku bar ni naje na rungumi ƙawata ina so na gode mata domin ta sanar dani cewa nayi zaɓen tumun dare."

user4590265594299 ya rubuta:

"Ta iya yiwuwa ba shine karon farko da suka kwanta tare ba, kuma ƙawar tayi niyyar ɓata mata aure. Ƴan baƙin ciki sun yi yawa."

Meyasa Zata Yi Min Wannan Ɗanyen Aiki? Magidanci Ya Koka Kan Halin Matarsa

A wani labarin na daban kuma, wani magidanci ya shiga takaici bayan ya gano matar sa ta ɓoye masa wani muhimmin sirri.

Magidancin dai yace sam bai yi tunanin haka halin mata yake ba, domin a cewar sa abinda matarsa tayi masa tsantsar mugunta ce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel