Hisbah ta Damke Malamin Islamiyya, Ana Zargin Shi da Laifin Lalata da ‘Dalibansa

Hisbah ta Damke Malamin Islamiyya, Ana Zargin Shi da Laifin Lalata da ‘Dalibansa

  • Ana zargin wani malami da laifin yaudarar daliban islamiyyarsa, yana yin lalata da su a gidansa
  • Mutane su na zargin mai dakin malamin take jawo masa mata zuwa gidansu domin ya yi fasikanci
  • Shugaban Hukumar Hisbah na Kano, Muhammad Harun Ibn Sina ya tabbatar da wannan labari

Kano - Hukumar nan ta Hisbah ta na bincike a kan wani malamin makarantar Islamiyya da ake tuhuma da laifin lalata da daliban makarantarsa.

Gidan rediyon Freedom ya rahoto cewa ana zargin wannan malami ya aikata wannan aika-aika ne a makarantar mahaifinsa wanda yanzu ya rasu.

Makarantar tana nan a unguwar Nasarawa a karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano.

Islamiyya mai yi wa addini hidima

Jaridar Aminiya ta ce wannan makarantar da malamin da ake jifa da zargin mummunan aikin yake koyarwa, ta yi suna wajen taimakon addini.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Bada Umurnin Tsare Magoya Bayan Atiku A Gidan Yari Har Sai Bayan Zaben Shugaban Kasa

A sakamakon rasuwar mai makarantar ne dalibansa suka dauki jagorantar islamiyyar. Wannan zai zama babban cin amana idan ta tabbata.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hisbah
Jami'an Hisbah a Kano Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Malami ya yi wa daliba ciki?

Kamar yadda labarin ya zo, mutane su na zargin abin ya yi kamari har malamin musuluncin ya bar daya daga cikin daliban da juna-biyu.

Da juna biyun ya bayyana ne sai malamin ya auri dalibar da ake magana, bayan haka kuma sai ta cigaba da kawo masa ‘yan mata zuwa gidansu.

Idan rahoton ya tabbata, matar malamin ta ke hada shi da daliban da zai rika lalata da su.

A cewar malamin da ba a iya bayyana sunansa ba, soyayya ce ta ke shiga tsakaninsa da ‘yan matan, daga baya sai ya bijiro masu da aikin assha.

Hukumar Hisbah ta samu labari

Da aka samu labarin irin barnar da wannan malami yake yi, sai magana ta kai wajen jami’an hukumar Hisbah wanda yanzu suka yi ram da shi

Kara karanta wannan

Canza Naira: Shugaban Majalisa Ya Sha Alwashin Daukar Tsattsauran Mataki Kafin Zabe

Muhammad Harun Ibn Sina wanda shi ne Shugaban Hisbah na reshen Kano ya ce sun samu labarin abin da yake faruwa, sai suka dauki mataki.

An rahoto Sheikh Harun Ibn Sina yana cewa gaskiya ta fara bayyana a sakamakon binciken na su.

Sarki a wasan kwaikwayo

A makon da ya gabata aka ji labari cewa Oonin Ile Ife watau Oba Adeyeye Ogunwusi, ya fito a wani fim na masana’antar Hollywood ta kasar Amurka.

A wannan fim na ‘Take Me Home’, Oba Adeyeye Ogunwusi ya fito matsayinsa na Basarake. Ana sa ran wasan kwaikwayon zai kayatar da jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng