Shawarwarin Masana Lafiya Dan Game Da Yanayin Sanyin Nan Da Ake Ciki

Shawarwarin Masana Lafiya Dan Game Da Yanayin Sanyin Nan Da Ake Ciki

  • A lokutan sanyi da dama jam'a na amfani da wasu hanyoyi domin dumama jikinsu ko kuma muhallin da suke zama a cikinsa
  • Wasu hanyoyin kan iya cutarwa ko kuma yin barazana ga muhallin nasu wajen gurbata yanayin sa
  • Ga wasu shawarwari da masana lafiya suka lalabu ga wanda yake bukatar ya magnace matsalar sanyi da ta addabeshi

A duk lokacin da aka ce watannin karshe dana sabuwar shekara sun tunkaro, to ba abinda yan Nigeria ke fuskanta musamman ma na yankin arewar kasar face tsananin sanyi, wanda yake zuwa da kura da hazo.

Hakan yasa wasu na amfani da hanyoyi da dama domin su dumama jikinsu ko kuma muhallin da suke zaune a ciki. Daga cikin hanyoyin akwai batun yin amfani da garwashi, ko kuma na'urar dumama daki ko shan shayi da dai sauransu.

Kara karanta wannan

Boka Ya Yi Mummunan Karshe, Ya Mutu a Wajen Lalata da Uwargidar Wani Fasto

Sanyi
Shawarwarin Masana Lafiya Dan Gane Da Yanayin Sanyin Nan Da Ake Ciki Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amfani da ire-iren wadan nan kan janyo illa ko nakasu ga lafiyar mutum ko muhallin da yake ciki. in ba ku manta ba kwanannan mun kawo muku rahoton yadda wasu magidanta suka rasa ransu sakamakon jin dumi

Healthguide sun fitar da wasu hanyoyi da suke ganin idan mutum ya bisu zai samu saukin jin sanyi a jikinsa ko a muhallinsa. Shawarwarin sune kamar haka:

1. Rufe Hanci da Baki In Zaka Fita

Lokacin hunturun sanyi akwai yaayin kura da isaka wanda rashin rufe su kan sa kurar ko iskar su shiga jikinka. hakan zai taimaka maka mutuka wajen kare dattiin da zai shiga jikinka.

Idan iska ta shiga jikinka da yawa to in ta waje ta bugeka zata motsa wadda ta shiga jikinka ne dan haka zakaji sanyi sosai.

Kara karanta wannan

Wanda Zai Gaji Shugaba Buahri Zai Tarar Da Bashin Da Zai Iya Danne Shi, Wanda Adadinsa Ya Kai Naira Tiriliyan 77

2. Yawan Motsi

Ana yawan samun kamfa ko bushewar gumi a jikinka wanda yake taimakawa wajen fitar da wasu cuttutukan. yawan mosti kan taimaka maka wajen yin gumi dan fitar da wannan dattin ko cutar.

Sannan ka lizimci shan ruwa sosai. Ko kuma wani abu mai ruwa-ruwa da baida illa a tattare dashi.

3. Cin Abinci mai kyau

Yawan cin abinci mai kyau, kamar kayan marmari da kuma wanda suke dauke da sinadarin Vitamin da Minerals na taikawa sosai wajen gina fatarka da kuma kareka da ga cuttukan da sanyi ke zuwa da shi.

4. Sa kayan da suka dace da lokacin

Yana da kyau mutum ya lura da irin kayan da yake sawa, ba koda yaushe ya kasance cikin sa kayan sanyi ba, da lokacin da akwai sanyin mai yawa ko kuma lokacin sanyin kadan ne.

5.Kula Da Yanayin fata

Da sanyi wasu zakaga fatarsu na yawan bushewa. yadda mutum zai magance wannan shine ya ringa amfani da mai akai-akai domin shafawa fatar tasa, wanda hakan zai taimakawa fatar wajen kin bushewa ko kuma tsagewa.

Kara karanta wannan

BUK: Dalibai Mata Sunga Tasku, An Shiga Har Dakunan Kwanan Su Anyi Musu Sata

6. Shan Leman Tsami Da Zuma

Yawan shan lemon tsami da zuma a ruwa mai dan dumi kan taikawa wajen tabbatar da yanayin jikinka ya daidaitu ba tare da ya daga ko ya sauka ba.

7. Samun Kulawa Masana Lafiya

Wasu na da cuttutuka na sanyi, kamar Asma, Nimoniya da dai sauransu. Muddin kasan kana da wata cuta da take tashi lokacin sanyi to kayi kokarin tuntubar likita ko masanin lafiya da zarar sanyi ya shigo dan samun shawara ko mafita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel