Barayi Sun Shiga Dakin Kwannan Dalibai Mata A Jami'ar Bayero Da Ke Kano

Barayi Sun Shiga Dakin Kwannan Dalibai Mata A Jami'ar Bayero Da Ke Kano

  • Dakin kwanan dalibai dai mata na samu tagomashin tsaro sosai akan na maza, sakamakon wanda suke zaune ko kwana a cikinsa, musamman ma a manyan makarantun sikandire dana gaba da ita
  • Akwai dakunan kwana dabam dabam na mata a jami'ar Bayero, wanda ake musu lakaqi ba da sunan wasu fiattatun mata kamar Ramat, Hasiya da sauransu
  • Barayin sun shiga "Nana Hall" ne inda suka yi mumunar barna satar wayoyi da ababe masu amfani.

Kano - Wata mai amfani da kafar sadarwa ta facebook kuma daliba a jami'ar tarayya ta BUk dake Kano, SUlaiman Khairat Jaruma ta rawaito a shafinta na facebook cewa barayi sun shiga dakin kwanan dalibai.

Ta ce barayin sun shiga dakin kwanann daliban ne da daddare yayin da dalibai matan ke bacci, tunda dare yayi sosai.

Kara karanta wannan

Daga Jin Dumi Ashe Karshensu Ne Yazo, Yadda Wasu yan gida suka rasa ransu

NANA HALL
Barayi Sun Shiga Dakin Kwannan Dalibai Mata A Jami'ar Bayero Da Ke Kano Hoto: UCG
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami'ar dai ta dawo daga hutun kirsimeti da sabuwar shekara a farkon satin nan da muke ciki wanda hakan yasa akwai karancin dalibai a hostel din.

Khairat ta ci gaba da cewa

"Wannan shine karo na biyar da nake zaune a Hostel da barayi ke shiga suyi sata"

Ta ci gaba da cewa :

"Ni abinda ya fi bani haushi shine yadda hukumar tsaron jami'ar suka ce wai muna ina har barayin suka shiga sukai satar bamu sani ba"
"To sai dai mun godewa Allah ba rauni ba jikkata ko kuma wata barazana"

Sharhin wanda suke binta a shafinsu

Kimanin mutane arba'in da doriya ne suka tofa albarkacin bakinsu kan yadda wannan al'amarin ya faru.

wani Beli Abubakar Nasiru yace:

"Wannan abu bai dadi ba, Allah ya kiyaye gaba, Allah ya tona musu asiri"

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kashe Dan Siyasa Da Wasu Mutane Uku a Wata Jahar Kudu

Abba Sauna Kawaji kuwa cewa yace

"Abun bakin ciki wallahi"

Shi kuwa Ahmed Umar cewa yace

"Maye alhakin jami'an tsaron jami'ar, shin mai aka dauke su suyi."

Nana Hauwa Iye Ahmadu kuwa tace

"Ni fa banga amfanin sa mata jami'an tsaro a hostel din nan ba fa, sabida basu da wani amfani, duk shekara ko kuma duk zangon karatu sai an samu wani abu makamancin haka"

An Kama wani Namiji Yayi Shigar Mata Ya Shiga Dakin Kwanan Dalibai A Jami'a

An kama wani tsoho da yayi kokarin shiga dakin kwanan dalibai mata a jami'ar Ahmadu Bello Dake Zaria kamar yadda wata ta wallafa a shafinta.

Salam malama yau kawai sai ga wani tsohon banza na kokarin shiga hostel dinmu (Ribadu Hall) a Samaru, wajen karfe hudu na asubh aka kamashi.

ga bidiyon nasa:

Asali: Legit.ng

Online view pixel