Wanda Zai Gaji Buhari Zai Sha Fama Da Bashi Kamar Ba Gobe

Wanda Zai Gaji Buhari Zai Sha Fama Da Bashi Kamar Ba Gobe

  • Tunda gwamnatin shugaba Buhari tazo take fama da cin bashi da cike gibin kasafin kudin da ta keyi duk shekara.
  • Ko kwanann nan ma shugaba Buhari ya aikea da majalissar Dattijai data Wakilai takardar neman sahalemasa ya ciwo wani bashin
  • Abin da masana ke korafi akai shine yadda ko an viyo bashin ba'a yin abinda ya kamata dashi sai dai wani abu can dabam

Abuja - Ofishin da ke kula da hada-hadar bashi na kasa ya bayyanawa yan Nigeria yadda bashin da babban bankin kasa yake bin gwamnatin tarayya da kuma yiyuwar barin wasu bashin da yakai naira tiriliyan 77.

A wannan laraba da ta gabata hukumar ta sanar da cewa wanda zai gaji shugaba Buhari kan iya tarar da bashin da yakai Tiriliyan 77, indan gwamnatin Buhari ta kare a watan mayun wannan shekarar

Kara karanta wannan

Yadda Matashi Ya Kera 'Motar Kara' Harda Sa Mata Injin, Ya Tashe Ta a Cikin Bidiyo

kiyasin na zuwa ne bayan da da hukumar ta gabatarwa da jama'a bayanin kudaden hukumar da kuma wasu sabbin dokoki da duka kankane hukumar wanda za'a aiwatar a wannan shekarar da muke ciki. Rahotan The Cable

Shugabar hukumar Patience Oniha tace bayyana bashin da ake bi da kuma yin wasu dokoki shine kawai hanya da zata dakatar da gwamnatin tarayya cin bashin.

MD Maaikatar
Wanda Zai Gaji Buhari Zai Sha Fama Da Bashi Kamar Ba Gobe Hoto: The Cable
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sannan tace akwai yiyiwar siyar da wasu kadarorin gwamnati dan samun kudin shiga, tana ganin sune hanya kawai da za'ai amfani da su wajen ciyar da Nigeria gaba.

Tace wannan hanyar zata taimakawa hukumarta ta samar da hanyar da za'a magance cin bashi da kuma tabbatar da bashin da aka ci din anyi abinda aka ci dominsa.

"Kalli yadda aka gudanar da aiyuka yanzu, gaba daya abinda ake bin gwamnatin tarayya fa, da sauran jihohi 36 in ka hada da kudin ruwa ya kai kusan tiriliyan 77"

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kashe Dan Siyasa Da Wasu Mutane Uku a Wata Jahar Kudu

"Kuma a yanzu ana shirin kara wasu basussukan da su ka kai kusan triliyan guda dan ganin an cike gibin kasafin kudin bana, wanda kuma tuni majalissar dokokin Nigeria ta sahale da karbar bashin"

Akwai kusan hasashen cewa za'a kashe kusan tiriliyan 5.67 da kuma karin wasu kudaden da ake sa ran za'a aro su wanda adadinsu ya kai tirliyan 11.34 kafin watan Mayun wannan Shekarar.

Mai za'ai Da Bashin

A cikin kudin da ake sa ran za'a ci bashin wanda jumularsa ta kai naira tiriliyan 1.5 akwai batun biyan ariyas ga ma'aikatan shari'a da kuma buga sabbin kudi.

A jumlance kudin ba iya gwamnatin tarayya ce zata ciyo bashin ba, hadi ne da gwamnatocin jihohi da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel