Mahaifi da Yaronsa Sun Hadu Sun Jibgi Ma’aikata Saboda Uwarsu Ta Rasu a Asibiti

Mahaifi da Yaronsa Sun Hadu Sun Jibgi Ma’aikata Saboda Uwarsu Ta Rasu a Asibiti

  • Wani mutumi tare da yaronsa ya dauki matarsa mara lafiya mai shekaru 53 zuwa asibitin FMC Idi-Aba
  • Da aka je asibitin tarayyar, likitoci sun ce ba a dade sosai ba sai ciwon zuciya ya kashe wannan mata
  • Ganin abin da ya faru sai mijin wannan mata da yaronta suka lakadawa likita da wata ma’aikaciya duka

Ogun - Wani fusataccen mutumi da yaronsa sun jibgi likita da wata ma’aikaciyar jinya a asibitin tarayya da ke Idi-Aba, Abeokuta a jihar Ogun.

Daily Trust ta ce ana zargin wadannan mutane biyu sun yi wannan danyen aiki ne a dalilin mutuwar mara lafiyarsu, wata ‘yar shekara 53 a Duniya.

Abin da ya faru shi ne, da wannan mutumi da yaronsa su ka kawo mara lafiyarsu sashen bada agajin gaggawa na asibitin, ba ta dade ba ta rasu.

Kara karanta wannan

Bakon Biki Ya Gwangwaje Amarya da Ango da Daurin Itace, Bidiyon Ya Ba Jama'a Mamaki

Ganin sun rasa mahaifiya da mata ya fusata yaron da mahaifinsa, haushi ya jawo suka yi ta bugun malaman asibitin har aka kira jami’an tsaro.

Magana ta kai ga 'yan sanda

Har ‘yan sanda suka zo, rahoton ya nuna wadannan mutane ba su daina bugun ma’aikatan lafiyar ba, yanzu maganar ta na hannun hukuma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar likitoci ta reshen jihar Ogun ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta ce mara lafiyar ta mutu ne a sakamakon bugun zuciya da tayi fama da ita.

Asibiti
Wasu likitoci na aiki a asibiti Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Daily Post ta rahoto shugaban NMA, Dr. Kunle Ashimi yana cewa an wuce da mutanen zuwa ofishin ‘yan sanda da ke Kemta domin a hukunta su.

Ashimi ya ce sunan likitan da aka yi wa wannan cin zarafi Dr. Pelumi Somorin, amma har zuwa yanzu ba mu da masaniya a kan ma’aikaciyar jinyar.

Ba za mu sake yarda da wannan ba - NMA

Kara karanta wannan

Rikici Kan Bazawarar Yan Bindiga Ya Janyowa Mutane Asarar Rayukan Mutum 69 a Zanfara

Kamar yadda Tribune ta fitar da rahoto, kungiyar Lauyoyi tayi gargadi ga mutanen Najeriya su kauracewa cin zarafin malaman lafiya da ke bakin aiki.

NMA ta ce duk wani da aka samu ya wulakanta malaman asibiti, doka za tayi aiki a kan shi.

“Mun yanke hukunci cewa wannan ne karon karshe da za a lallashe mu. Mun dauki matsaya za mu je kotu, za mu hadu a gaban kuliya gobe.
Mun fara duk wani shirye-shiryen shari’a, kuma za mu kai maganar zuwa gaban Alkali. Duk girman mutum, za muyi shari’a da shi a kotu.”

- Dr. Kunle Ashimi

Akanta ya saci N34m a FCE

Kun ji labari satar N34m ta jawo wani Akanta da aka yi a FCE Eha-Amugu a garin Isi-Uzo a Enugu, zai yi fiye da shekaru 300 yana garkame a gidan yari.

Tun a shekarar 2010 ake shari’a tsakanin Emmanuel Sombo da Lauyoyin EFCC a kan zargin ya saci Naira Miliyan 34.5 daga asusun makaranta a Enugu.

Kara karanta wannan

Abin takaici: An yi jana'izar wasu ma'aurata da 'yan bindiga suka kashe bayan karbe kudin fansa N7.5m

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng