Yadda Dangin Mijina Suka Umurci Ɗayansu Ya Gaje Ni Bayan Rasuwarsa, In Ji Matar Yar Jihar Arewacin Najeriya

Yadda Dangin Mijina Suka Umurci Ɗayansu Ya Gaje Ni Bayan Rasuwarsa, In Ji Matar Yar Jihar Arewacin Najeriya

  • Har yanzu akwai garuruwa a Najeriya inda suke da al'adu masu ban mamaki ciki har da yin gadon matan yan uwansu idan sun mutu
  • Wata mata yar asalin jihar Benue, ta magantu kan yadda yan uwan mijinta suka bukaci wani cikin dangin ya gaje ta bayan mutuwar mijinta
  • Perpetua ta bayyana wasu kallubale da ta yi karo da su kamar rashin bata gado da sauransu duk bayan rasuwar mijin nata kimanin shekaru tara da suka shude

Perpetua Oche, mata wacce ta rasa mijinta shekaru tara da suka gabata lokacin suna zaune a jihar Legas, ta bayyana labarinta game da 'gadon mata', al'adar da har yanzu ana yi a wasu sassan kasar.

Oche, a hirar da Daily Trust ta yi da iya ta ce ta sha wahalhalu da kallubale da dama bayan rasuwar mijinta.

Kara karanta wannan

An Kama Saurayi Da Budurwa Kan Binne Jinjirinsu Da Ransa A Wata Jahar Arewa

Perpetua Oche
Bayan Mutuwar Mijina, An Nemi Wani Dan Uwansa Ya Gaje Ni, Matar Da Mijinta Ya Rasu A Benue. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A halin yanzu ta zama mai magana da yawun mata wadanda suka rasa mazajensu tana amfani da muryarta don kira ga hukumomi su kawo karshen wannan al'adar mara kyau.

Ta fara da cewa:

"Daga jihar Benue na ke - kabilar Idoma, amma mijina dan jihar Delta ne. Ya rasu shekaru tara da suka shude. Bayan mijina ya rasu a Agustan 2013, ba a birne shi ba sai bayan wata shida."

Al'adun da aka yi bayan rasuwar mijina

Parpetua ta cigaba da cewa:

"Bayan an birne mijina a 2014, an fada min za a yi wasu al'adun gargajiya. Dattawa suka taru aka sa ni a tsakiya tare da ya ta, sai aka fada min zan auri daya cikin danginsa. Amma, kafin nan, Allah ya yi amfani da daya cikinsu ya fada min abin da zai faru don haka da suka fada min, na amsa da cewa ba zan iya yin hakan ba.

Kara karanta wannan

Amimu ya shaki iskar 'yanci: Yadda aka mika matashin ga iyayensa daga magarkama

"Sai suka ce idan ba zan amince ba zan dawo musu da kudin sadaki. Iyaye na sun fada min kada in yi jayayya da su, sai na tambayi nawa ne sadakin."

Kamar yadda rahoton na Daily Trust ya rahoto, ta cigaba da cewa:

"Daga nan suka tambayi wanda ake son ya gaje ni nawa zan biya, sai ya fadi wani adadi amma matan gidan suka ce a'a, kudin ya yi yawa. Sai ya ambaci wani kudin da na ke da shi a jiki na, sai na fito da shi na mika masa.
"Bayan nan, dattijo mafi shekaru a iyalin ya mana addu'a ni da ya ta suka kyalle mu muka tafi. Sun bukaci mu siya lemun kwalba wanda dattawa za su sha, sai suyi mana addu'a."

Rasuwa bayan mijina

Perpetua ta ce kowa ya juya mata baya, ita da surukanta da yar ta suke zama kuma ita ke yin dukkan aikin gida ga shi tana da karamar yarinya.

Kara karanta wannan

Talaka ya yi nasara: Abin da 'yan Najeriya ke cewa bayan da Aisha Buhari ta janye kara kan Aminu

"Daga baya na fada wa suruka ta zan koma garin mu, ta ce dole sai na rubutu mata adireshin gidan mu da lambobin wayan yan uwa na kuma sai na yi alkawarin zan rika kawo yarinyar lokaci zuwa lokaci. Na yarda da hakan daga bisani ta bari na tafi."

An baki gado?

"Aa'a, ba su bani gado ba, bana son ma su bani. Bana son a yi min gori."

Menene ra'ayin ki kan kudirin dokar hana tsangwamar matan da mazansu suka mutu a jihar Benue?

"Kudirin doka ne mai kyau. Dukkan duniya za ta san cewa ana irin wannan abin da ya kamata a dena kuma mata ba su iya kare kansu su nemi hakkinsu. Fahimta na wannan dokar shirin irinsa na farko a Benue a Najeriya. Duniya za ta san abin da muke kuka kan wannan al'adun masu cutarwa."

Matar Da Ta Auri Maza Biyu Kuma Suna Zaman Lafiya

Kara karanta wannan

Cika alkawari: Tela ta saka amarya kukan dadi bayan da ta cika alkawari, ta gwangwaje ta

A wani rahoton, wata baiwar Allah a kasar DRC Congo ta aikata wani abu da ba a saba gani ba a yankin Afirka wata auren maza biyu.

A harshen turanci ana kiran wannan irin auren da suna 'Polyandry' inda mace daya ke auren maza fiye da daya kuma a wannan karon gida daya suke zaune.

Asali: Legit.ng

Online view pixel