Matar Mutum: Yadda Masoya Suka Dawo Aka Yi Aure Bayan Shekaru 2 Ba a Tare

Matar Mutum: Yadda Masoya Suka Dawo Aka Yi Aure Bayan Shekaru 2 Ba a Tare

  • Akwai abin ban sha’awa a labarin soyayyar Ibrahim Adam da kuma masoyiyarsa, Aisha Abdulrahman Haruna
  • Ibrahim Adam yace bayan shekaru biyu da rabuwa da Aisha, wata rana sai ya yi kuskuren kiran lambar wayarta
  • Kamar wasa haka alaka ta dawo danya, aka busawa tsohuwar soyayya rai, yanzu sun zama amare da ango a Kano

Kano - Hausawa suna cewa da tsohuwar zuma ake yin magani, abin da ya faru kenan tsakanin Ibrahim Adam da Aisha Abdulrahman Haruna.

A shekarun baya, Ibrahim Adam da Aisha Abdulrahman Haruna suna tsakiyar soyayyarsu, sai kurum sabani ya shiga tsakani, don dole suka rabu.

Kamar yadda Ibrahim Adam ya bada labari a Facebook, shekaru kusan biyu bayan ya rasa igiyar soyayyar Aisha Abdulrahman, sai ta dawo rayuwarsa.

Yadda abin ya faru shi ne, wata rana ya dauko waya zai kira ‘yaruwarsa mai suna Aysha, sai kaddara ta sa ya rangadawa tsohuwar buduwarsa waya.

Kara karanta wannan

Soyayya Ruwan Zuma: Dattawan Da Suka Shafe Shekaru 51 Da Aure Sun Girgiza Intanet, Bidiyonsu Ya Burge Matasa

Ibrahim ya kira takwarar 'yaruwarsa

Ko da suka yi magana ta wayar salular, sai Malama Aisha Abdulrahman Haruna tace Allan-barin ta manta da wani mai suna Ibrahim Adam a Duniya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daga nan ta bukaci ya turo mata hotonsa ta dandalin WhatsApp, kuma hakan aka yi. Matashin yana ganin wannan duk jan aji ne kurum na ‘yan mata.

Auren soyayya
Hoton auren Ibrahim Adam da Aisha Abdulrahman Haruna Hoto: @Ibraheemz01
Asali: Facebook

An hadu a WhatsApp

Watakila daga tura mata hoton na sa ne sai wannan Baiwar Allah ta canza shawara, yanzu maganar da ake yi, tayi mako biyu a matsayin Amaryar Ibrahim.

Da yake bada labarin soyayyarsu a shafinsa, wannan matashi ya nuna tattaunawar farko da suka yi bayan rabuwarsu, an yi haka shekara daya da ta wuce.

A ranar 25 ga watan Nuwamban 2022, aka daurawa Ibrahim Adam aure da sahibarsa, Aisha Haruna a wani masallaci a unguwar Kofa mata da ke garin Kano.

Kara karanta wannan

Gwamnan Babban Jihar Arewa Ya Faɗa Wa Ƴan Najeriya Wanda Ya Cancanta Su Zaɓa Shugaban Kasa A 2023

Yayin da Malam Aisha take gidan Malam Ibrahim, muna yi masu addu’ar zaman lafiya da albarka.

Kamar yadda wani ya fada, ‘yan mata da samari su rika bibiyar tsofaffin masoyansu domin kuwa za a iya dacewa, dama an ce da tsohuwar zuma ake magani.

Naja’atu Mohammed vs Aisha Buhari

A wata hira da aka yi da ita, an ji labari Hajiya Naja’atu Mohammed tayi kaca-kaca da Mai dakin Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari a kan tsare matashi.

Naja’atu Mohammed tace a baya Aisha Buhari ta taba yin irin haka, ta bada umarni ga jami’an tsaro su lakadawa dogarinta duka, wanda hakan bai dace ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel