Jami’an ‘Yan Sanda Sun Cafke Wasu Mutum 2 da Suka Yi ‘Fashi’ da Bindigogin Roba

Jami’an ‘Yan Sanda Sun Cafke Wasu Mutum 2 da Suka Yi ‘Fashi’ da Bindigogin Roba

  • ‘Yan Sanda sun kama wasu mutane da ake zargin sun shiga shago da nufin suyi fashi da makami
  • Ana tuhumar mutanen biyu da yin amfani da bindigogin karya domin su karbe dukiyar jama’a
  • Da samun labarin abin da ke faruwa, jami’an tsaro suka tura runduna da ta cafke su tsamo-tsamo

Ogun - Jami’an ‘yan sanda na reshen jihar Ogun, sun damke wata mata da wani saurayi da laifin yin fashi a unguwar Adesan da ke yankin Mowe.

Abin ban mamaki tattare da rahoton na Daily Trust shi ne ana zargin da bindogin roba wadannan mutane biyu suka nemi suyi wa Bayin Allah fashi.

Kakakin ‘yan sanda na Ogun, Abimbola Oyeyemi ya shaidawa manema labarai sun samu labari, daga nan suka yi maza suka kama mutanen da ake zargi.

Kara karanta wannan

Osun: Rikicin Sarauta ya Barke, An Bindige Yarima Lukman Har Cikin Fada

Wadanda ake zargi sun shiga shagon Johnson Nwokoro inda ake saida abinci a yankin Adesan, kuma suka karbe cinikin ranar da aka yi a shagon.

'Yan sanda sun yi kokari

Da jami’an tsaron suka ji labari wasu ‘yan fashi sun auka shagon wani mai suna Johnson Nwokoro, nan-take DPO, SP Folake Afeniforo ya dauki mataki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kafin a kai ko ina, dakarun da Folake Afeniforo ya tura sun isa shagon da ake neman yi wa fashi da makamai, kuma aka yi nasarar cafke mutanen nan biyu.

'Yan fashi
Chioma Okafor da Nweke Joshua Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

An bada sunayen wadanda ake tuhuma a matsayin Chioma Okafor mai shekara 29 da kuma wani saurayi ‘dan shekara 19 a Duniya, Nweke Joshua.

Shawarar Chioma Okafor ce - Nweke Joshua

Daily Post ta rahoto Joshua yana mai cewa matar ta bada shawarar suyi fashi domin sus amu kudi, kuma ita ta kawo bindigogin da suka yi amfani da su.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: ISWAP ta kai kazamin hari kan sansanonin soji a Borno, an hallaka sojoji da yawa

"Yayin da aka lalube jikinsu, sai aka fahimci sun zo yin fashin ne da bindigogin roba da suka yi kama da karamar bindigar gaske.
Da aka yi masu tambayoyi, Nweke Joshua mai shekara 19 ya shaidawa ‘yan sanda cewa Chioma Okafor ta kawo wannan shawara.
Da suka je shagon sai suka yi kamar sun zo yin sayayya ne, kwatsam sai suka fito da bindigogi, suka bukaci a ba su kudin da aka adana.
Kashinsu ya bushe lokacin da rundunar ‘yan sanda suka duro wurin kafin su iya tserewa.”

- Abimbola Oyeyemi

Sauke shugaban NYSC

Kun ji labari babu mamaki Birgediya Janar Muhammad K. Fadah yana cikin Shugabannin hukumar NYSC da ba su dade ko kadan a kujerar DG ba.

Tuhumar Muhammad Fadah da amfani da takardu da shekarun bogi da kuma laifin son kai da rashin sanin makaman aiki suka jawo ya rasa kujerarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng