An Bindige Yarima Har Fada Yayin da Rikicin Sarauta Ya Barka a Osun

An Bindige Yarima Har Fada Yayin da Rikicin Sarauta Ya Barka a Osun

  • Hankula sun tashi yayin da rikicin sarauta ya barke a yankin Ikirun na karamar hukumar Ifelodun dake Osun inda aka bindige yarima har fada
  • An gano cewa, fusatattun ‘yan gidan sarautar sun hana sabon sarki shiga fada inda suka cika ta da layu, lamarin da ya kawo ‘yan sanda
  • Sai dai cike da rashin sa’a, Yarima ya jagorancI matasa domin hana ‘yan sanda shiga fadar wacce aka bankawa wuta, amma ‘yan sanda suka harbe shi

Osun - An samu faruwar tashin hankali a yankin Ikirun, hedkwatar karamar hukumar Ifelodun ta jihar Osun a ranar Laraba yayin da jami’an tsaro suke neman kutsawa fada amma suka harbi Yarima Lukman Gbeleru.

Taswirar jihar Osun
An Bindige Yarima Har Fada Yayin da Rikicin Sarauta Ya Barka a Osun. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Jaridar The Nation ta rahoto cewa, an dinga zanga-zanga sakamakon nada Oba Yinusa Akadiri da aka yi matsayin sabon basaraken yankin inda aka harbe mutum biyar.

Kara karanta wannan

Bincike Kan Balle Magarkamar Kuje ya Kammala, Ba Zamu Fitar Bane, Minista

Fusatattun ‘ya’yan gidajen sarautar sun garkame fadar tare da zuba layu domin hana sabon basaraken shiga.

A safiyar Laraba, jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda sun dira fadar inda suka nemi shiga farfajiyar, lamarin da yasa matasa suka hana cike da tarzoma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar ThisDay ta rahoto cewa, wani mazaunin yankin da ya bukaci a boye sunansa, yace ‘yan sanda sun kutsa tare da shiga fadar amma wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun bankawa fadar wuta.

Yariman da ya dinga hana jami’an tsaron shiga fadar ta karfi da yaji an harbe shi.

Wata majiya tace masu kashe gobara uku suka hallara a fadar amma aka raunata su yayin da suke kan hanya. Dole tasa suka bar abun hawansu.

Yarima Tajudeen Gboleru ya sanar da The Nation cewa:

“An halaka ‘dan uwana a yayin wani fada a gaban fada a safiyar yau. Ya jagoranci wasu matasa zuwa fada yayin da yaji za a shiga fadar, tarzoma ta tashi yayin da wani ‘dan sanda ya harbe shi.”

Kara karanta wannan

Mutum 23 Sun Yanke jiki sun Fadi Yayin Tattakin Goyon Baya ga Tinubu da Shettima a Kano

Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Osun, Ibrahim Adekunle, ya tabbatar da cewa an raunata mutum uku cikin jami’ansu a Ikirun kan hanyarsu ta zuwa kashe gobara a fadar Ikirun da safe.

“Ina kan hanyata ta zuwa asibiti yanzu.”

- Yace.

Yan daba sun kai hari majalisar Bauchi

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa wasu ‘yan daba da ba a san ko su waye ba sun kai farmaki majalisar jihar Bauchi.

Miyagun sun raunata mutum shida inda suka yi yunkurin bankawa majalisar wuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel