Tirkashi: ‘Yan fanshi da Barayi Sun sace Wayoyi 76 da Kayan kusan N5m
- Kazeem Bamidele yana kotu ana shari’a da shi tare da wasu mutanen da sun tsere, ana tuhumarsu da satar wayoyi a yankin Ajegule
- Ana kuma zargin wannan mutumi mai shekara 50 ya saye wata wayar iPhone 12 Pro Max a kan N520,000 amma ya karyata zargin
- An kuma maka wani Wasiu Adele a wani kotun majistare na Ogba a jihar Legas, ana zarginsa da satar kaya da rike kudi na bogi
Lagos - Wani mutum mai shekara 50 a Duniya, Kazeem Bamidele ya bayyana a gaban kotun majistare ta garin Ikeja a jihar Legas, ana zarginsa yin sata.
Rahoton da ya fito daga Punch a ranar Laraba, 24 ga watan Agusta 2022, ya nuna cewa ana tuhumar Kazeem Bamidele da laifin satar wayoyin salula.
Ana tuhumar Bamidele da wasu da ba a kama ba da zargin aikata laifuffuka biyar da suka hada da daukar kayan da ba na su ba, da makamantan haka.
Kamar yadda rahoton ya bayyana, Lauyoyi sun fadawa karamin kotun na majistare cewa har yanzu ba a kai ga kama sauran abokan aikin Bamidele ba.
Laifuffukan da aka karantowa mutumin sun hada da sayen wayar wata iPhone a kan N520, 000.
Sayen iPhone 12 Pro Max ta sata
“Ana zargin kai Kazeem Bamidele wanda aka fi sani da Elewure da wasu da ake nema, sun karbi wata wayar iPhone 12 pro max ta wani mai suna Ojobaro Michael a kan N520,000.00.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wannan ya faru a ranar 9 ga watan Yuli 2022 da kimanin karfe 10.30 na dare a Ajegunle a yankin Ajeromi da ke jihar Legas.”
Sauran laifuffukan da ke wuyan Kazeem Bamidele
“Ana zargin kai Kazeem Bamidele wanda aka fi sani da Elewure da wasu da ake nema, kun sace nau’o’in wayoyi 76 daga wajen mutane.
Wannan ya faru a ranar 9 ga watan Yuli 2022 da kimanin karfe 10.30 na dare a Ajegunle a yankin Ajeromi da ke jihar Legas.”
Bayan wanda ake zargi ya fadawa kotu bai aikata laifin ba, an bada belinsa a kan N500,000 tare da jingina. An kuma daga lokacin cigaba da shari’ar.
Ana haka sai aka ji ana shari’a a kotun majistare na Ogba da Wasiu Adele mai shekara 42 da laifin amfani da kudin bogi da satar kayan N4.8m.
Taron NBA a Legas
Kun ji an gayyaci Atiku Abubakar, Bola Tinubu, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso suyi jawabi, sannan wasu ‘Yan takaran Shugaban kasa sun samu zuwa.
‘Dan takaran NNPP, Kwankwaso ne bai amsa gayyatar Shugaban NBA ba, kuma bai turo akalla wanda zai wakilce shi domin ya fito da manufofinsu ba.
Gaskiya ta Fito: Sojan da Ya Halaka Sheikh Aisami an Sauya Masa wurin AIki ne Saboda Yayi wa Kwamanda Sata
Asali: Legit.ng