Garkuwa da mutane: Alkali ta yanke hukunci a kan Budurwar da tayi karyar an sace ta
- An yi shari’a tsakanin Ameerah Sufyan da Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya a wani kotun majistare
- Da aka zauna a gaban Alkali, Ameerah Sufyan ta amsa laifuffukan da ake zargin ta da aikatawa
- Alkali ta yi hukunci cewa sa'ilin da Budurwar ta yi wannan aiki, ba ta da cikakkiyar lafiya kwakwalwa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Dazu wani karamin kotun majistare da ke zama a unguwar Wuse 2 a garin Abuja, ya saurari kara a kan wata Ameerah Sufyan mai shekara 23.
Wannan Baiwar Allah ta kitsa labarin cewa an yi garkuwa da ita, alhali ba ta hannun ‘yan bindiga. A kan haka ne ‘yan sanda suka kai kararta a kotu.
Rahoton da jaridar Punch ta fitar dazu, ya tabbatar da cewa Sufyan ta amsa laifin ta da bakinta.
Da ta bayyana a gaban Alkali Chukwuemeka Nweke a ranar Laraba, 29 ga watan Yuni 2022, Ameerah Sufyan ta amsa duka zargin da suke wuyanta.
Jami’an ‘Yan sandan Najeriya su na zargin wannan mazauniyar unguwar Apo da laifin yi wa al’umma karya da fitar da bayanan da za su yaudari jama’a.
Hukuncin Alkalin kotu
Da take zartar da hukunci a zaman da aka yi, Mai shari’a Nweke ta ce ya saki Sufyan tare da la’akari da sashe na 454 na dokar ACJA ta shekarar 2015.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda Alkalin ta zartar, idan aka duba takardar lafiyar da aka gabatar, yarinyar ba ta cikin cikakken hayyacinta a lokacin da ta yi wannan danyen aiki.
A dalilin haka Alkalin ta ce dole a sa wa wanda ake tuhuma ido har na tsawon watanni 12.
Daily Nigerian ta ce kotu ta yanke hukunci a za a saki wanda ake zargi da sharadin kawo wanda zai tsaya mata, kuma za a rika lura da kai-komonta a kullum.
Jami’ar ‘yan sandan da aka bada domin ta sa wa Sufyan ido ita ce DCP Hauwa Ibrahim.
Baya ga haka, Mai shari’a ya ce a kowane wata sai wannan budurwa ta je babbar hedikwatar ‘yan sanda da ke garin Abuja domin a rika duba halin da ta ke ciki.
Lauyar da ta tsayawa budurwar, Chinyere Moneme ta gamsu da hukuncin daaka gabatar da kuma karar da ‘yan sanda suka shigar ta hannun James Idachaba.
Labarin satar mutane na karya
Ku na sane da cewa kwanakin baya Ameerah Sufiyan ta fito shafin Twitter tana cewa an yi garkuwa da su a Abuja, bayan kwanaki uku, gaskiya ta bayyana.
‘Yan Sanda sun gano Ameerah Sufiyan, an kuma tabbatar da cewa ba dauke ta aka yi ba. Bayan nan bayanai su ka rika fitowa cewa ta na da matsalar kwakwalwa.
Asali: Legit.ng