Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Najeriya Ta Dauki Hayan Lauyoyi Da Za su Kare Ekweremadu Da Matarsa

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Najeriya Ta Dauki Hayan Lauyoyi Da Za su Kare Ekweremadu Da Matarsa

  • Ahmad Lawan, Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya ya ce sun gwamnati ta dauki lauyoyi don kare Ekweremadu da matarsa da ake zargi da yunkurin cire kodar wani
  • Lawan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba lokacin da ya ke tsokaci kan taron sirri da suka yi gabanin fara zaman majalisa na ranar
  • Lawan ya ce za su cigaba da aiki tare da ofishin jakadancin Najeriya da ke Birtaniya da Ma'aikatar Harkokin Kasashen Waje don ganin an yi adalci kan batun zargin da ake yi wa takwararsu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Shugaban Majalisa, Ahmad Lawan, a ranar Laraba ya bayyana cewa ofishin jakadancin Najeriya a Birtaniya ta dauki hayan lauyoyi da za su kare Sanata Ike Ekweremadu da matarsa da a yanzu ke tsare kan zargin cire sassan jikin mutum.

Kara karanta wannan

Cikakken jerin Sanatoci 58 da aka zazzage, ba za su koma kujerunsu a Majalisar Dattawa ba

Mr Lawan, ya bayyana hakan a ranar Laraba, yayin da ya ke bada bayani kan taron sirri da aka yi kafin fara zaman majalisar na ranar.

Ekweremadu da matarsa Beatrice.
Gwamnatin Najeriya Ta Dauki Hayan Lauyoyi Su Kare Ekweremadu Da Matarsa. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

A cewar Lawan, wata tawaga daga kwamitinta na harkokin kasashen waje za ta bar Najeriya zuwa Landan a ranar 1 ga watan Yulin 2022, don ziyartar sanatan, rahoton Daily Nigerian.

Lawan ya kara da cewa sun yanke shawarar saka baki kan halin da Ekweremadu ke ciki ne bayan sun tattauna da ofishin jakadancin Najeriya a Landan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa majalisar za ta tuntubi Ma'aikatar Harkokin Kasashen Waje da Ofishin Jakadancin Najeriya a Landan kan kama Sanata Ike Ekweremadu da yan sandan Birtaniya suka yi.

Ya ce:

"Na tattauna da jakadan mu a Birtaniya, Alhaji Isola Sarafa, wanda ya tuntubi takwararmu, wanda ya tura tawagarsa kotun Uxbridge inda aka kai Ekweremadu.

Kara karanta wannan

Kuma dai: Yan bindiga sun sake sace wani limamin Katolika a jihar Edo

"Ofishin jakadancin ta dauki wasu lauyoyi da za su kare takwararmu.
"Mun yaba musu kan matakin da suka dauka. An tuntubi Ministan Harkokin Kasashen Waje, don ma'aikatar ta bada tallafi ga takwararmu."

Lawan ya kuma ce saboda batun na kotu ba za su iya daukan matakin da ya fi hakan ba a yanzu amma ya ce za su cigaba da hadin gwiwa da ofishin jakadancin don tabbatar da ganin an yi adalci.

Zargin Cire Sassan Mutum: Jami'ar Lincoln A Birtaniya Ta Yi Hannun Riga Da Ekweremadu

A bangare guda, Jami'ar Lincoln ta hana tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu cigaba da aikinsa a matsayin farfesa mai kai ziyara bayan zarginsa da safarar yaro dan shekara 15 zuwa Birtaniya don cire kodarsa, rahoton Channels Television.

A halin yanzu, Mr Ekweremadu da matarsa, Beatrice suna tsare hannun hukuma a Birtaniyan kan zargin, suna jiran shari'a a ranar 7 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Zargin Cire Sassan Mutum: Jami'ar Lincoln A Birtaniya Ta Yi Hannun Riga Da Ekweremadu

Dukkansu biyu sun musanta zargin da ake musu na safarar mutum.

Asali: Legit.ng

Online view pixel