Zamfara: An biya kudi, an saki 'yan kasuwan da aka yi garkuwa da su wajen daurin aure
- Mutanen nan da aka dauke a hanyar zuwa daurin aure a Zamfara sun samu ‘yanci a makon nan
- Sakataren kungiyar ‘yan kasuwan waya na Bebeji ya tabbatar da cewa an saki abokan aikin na su
- A karshe ‘yan bindigan da suka yi garkuwa da su, sun nemi a biya N400, 000 a kan kowane mutum
Zamfara - Mutum 29 da aka dauke a hanyar zuwa wani daurin aure a jihar Zamfara sun samu ‘yanci bayan kwana da kwanaki a hannun ‘yan bindiga.
A jiya wani wanda yake kusa da wadanda aka dauka, ya shaidawa gidan talabijin na Channels TV cewa wadannan Bayin Allah sun bar hannun ‘yan bindiga.
Ashiru Zurmi wanda Sakataren kungiyar ‘yan kasuwan waya ne ya shaidawa manema labarai cewa abokan aikin na sa sun samu ‘yanci, za su koma gidajensu.
A lokacin da aka zanta da shi, ya ce matasan da aka dauke su na hnayar su ta zuwa garin Gusau.
Su na hanyar zuwa Gusau
“Mutanenmu sun samu ‘yanci a yau, ina mai tabbatar maku da wannan. Yanzu haka su na kan hanyar zuwa garin Gusau.” - Majiya
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A hirar da aka yi da shi, Zurmi bai bayyana adadin kudin da ‘yan kungiyarsa ko ‘yanuwan wadannan Bayin Allah suka biya a matsayin kudin fansa ba.
An ce kowa ya biya N400, 000
Majiyar ta iya fadawa gidan talabijin cewa wadannan mahalarta daurin aure sun fito ne kurum. Premium Times ta ce sai da aka hadawa ‘yan bindigan kudi.
Abdullahi Lawal wanda ‘danuwansa na cikin wadanda aka dauke, ya ce sai da ‘yanuwa suka tara N330, 000, sannan abokan aikinsa suka tattaro ragowar kudin.
A cewar Lawal, ‘yan bindigan sun bukaci kowane dangi su tanadi N400, 000. Wasu sun iya hada wannan kudi, su dai ba su iya hada duk abin da aka nema ba.
‘Yan kasuwan sun shafe kwanaki kimanin 13 su na hannun ‘yan bindiga a jeji, tun bayan da aka tare su a kauyen Dogon Awo da ke tsakanin Tureta da Bakura.
A lokacin an bukaci a biya Naira miliyan 145 kafin a fito da su. Gwamnatin Zamfara ta yi alkawarin za ta yi bakin kokarinta na ganin an ceto mutanen.
An dauke mutane a Kaduna
Ana da labarin 'yan bindiga sun dauke mutane a Kaduna, inda aka shiga gidan wani Soja Unguwar Millenium CIty, aka dauke Uwargidar Jami’in tsaro.
Saura kiris a tafi da wata karamar yarinya tare da mahaifinta, amma ‘yan bindigan sun kutsa wani gida inda suka tattara masu gidan da wasu ‘yan mata biyu.
Asali: Legit.ng