Latest
Hukumar jin kai ta NASSCO ta ware talakawa miliyan 68 a jihohin Najeriya 36 da birnin tarayya Abuja domin raba musu tallafi domin yaki da talauci a Najeriya.
Majalisar dattawa ya bayyana takaicin yadda ake ci gaba da samun matsalolin tsaro a sassan kasar nan, wanda ya sa ta gayyaci shugabannin tsaro su bayyana a gabanta.
Jam'iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa maganar cewa akwai shirin sake tsayar da Goodluck Ebele Jonathan takarar shugaban kasa ba ta da tushe ballantana makama.
An yi martani ga gwamnatin tarayya kan neman bude makarantu a wasu jihohin Arewa a watan Ramadan. Dr Aliyu Tilde ya ce ba za a yarda da dakatar da hutun ba.
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed ya sanar da rasuwar kawunsa kuma Sarkin Alkaleri, Alhaji Muhammadu Abdulkadir, wanda ya rasu yana da shekaru 100.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ya gaya wa Buhari shirinsa na barin APC kuma sai da ya amince sannan ya koma SDP.
Rundunar 'yan sandan kasar nan ta yi nasarar hallaka matashin dan ta'adda, Dogo Saleh, wanda aka hakikance ya jawo asarar rayukan jama'a da dama bayan garkuwa da su.
Rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaron da ke cikin ayarin Gwamna Babagana Umaru Zulum sun fatattaki ƴan Boko Haram da suka tare matafiya a Borno.
Rundunar tsaro ta dakile harin ramuwar gayya na ‘yan bindiga a Mada, karamar hukumar Gusau, jihar Zamfara inda ta yi nasarar hallaka hatsabibin dan ta'adda.
Masu zafi
Samu kari