Latest
Wani mutum ya jawo cece-kuce yayin da ya jawo akuya a kasa, shi kuwa yana cikin mota bas. Ya ja akuyar a waje ne sadda aka hana shi shiga da ita cikin motar.
Allah ya yiwa matar Alh. Aminu Dantata, hamshakin attajiri kuma dattijon kasa rasuwa. Hajia Rabi Dantata ta rasu ne a Saudiyya bayan fama da rashin lafiya.
Tsohon sanata a Najeriya ya bayyana matsayarsa game da wanda ya kamata a zaba a ba shugabancin majalisar dattawa a wannan karon bayan saukar Ahmad Lawal a gaba.
Allah ya yi wa tsohon Antoni Janar na kasa kuma tsohon alkalin kotun kasa da kasa, ICJ, Bola Ajibola, rasuwa. Marigayin ya koma ga mahallincinsa yana shekara 89
Bola Tinubu da yake ketare zai dawo Najeriya saboda siyasar majalisa. Masu neman shugabancin majalisar dattawa sun hada da Jibrin Barau, Sani Musa, da Orji Kalu
Kungiyar Obi-Datti ta jam'iyyar LP ta ce dan takarar mataimakin shugaban kasarta, Datti Baba-Ahmed, ya shirya tsaf don yin muhawara da Farfesa Wole Soyinka.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya biya wasu daga kudaden da ake bin Najeriya bashi, ya sake cin wasu kudaden masu yawan gaske a shekarar da ta gabata ta 2022.
Bidiyo ya nuna yadda wani makaho ya bayyana neman auren wata kyakkyawar budurwa da ya dade suna tare suna abota. Ya fadi yadda yake ji game da ita a soyayya.
Jam'iyyar APC ta zargi wani sanatan jihar Taraba da cin dunduiniyarta a zaben da ya kammala a watannin da suka gabata. An bayyana dalilin dakatar da sanatan.
Masu zafi
Samu kari