Latest
Masu garkuwa da suka sace wata likitar ido, Ganiya Olawale-Popoola da mijinta Nuruddeen Popola da wani karamin yaro Folaranmi sun nemi naira miliyan 100 kudin fansa.
Ana fama da kudin man fetur a wajen kai yara karatun boko, Nyesom Wike ya kara haraji. Karin kudin da aka yi zai fara tasiri ne daga watan Junairun 2024.
Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya koka kan yadɗa rikicin siyasar jihar Ribas ya zame masa karfen kafa, ya hana shi zama cikin farin ciki da iyalansa.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai sabon farmaki a jihar Kaduna inda suka tafka sabuwar ta'asa. 'Yan bindigan sun yi awon gaba da wata matar aure da 'ya'yanta uku.
Dan takarar gwamna a jam'iyyar APC a jihar Anambra, Sanata Ifeanyi Ubah ya ce wa'adi daya kacal ya ke bukata ya daura jihar kan turbar ci gaba da tattalin arziki.
Wani dattijo da aka gano yana aikin neman na kai duk da cewar a duke yake tafiya ya samu kyautar kudi sama da naira miliyan 17 daga wajen yan Najeriya.
Majalisar dokokin jihar Edo ta ɗauki mataki kan wani ɗan majalisa ɗaya yayin da ta sahalewa Gwamna Godwin Obaseki ya karɓo bashin makudan kuɗi don yin ayyuka.
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi awon gaba da wasu yara ‘yan makaranta da ba a tantance adadinsu ba a karamar hukumar Emure da ke jihar Ekiti.
Shahararren mawakin nan na Najeriya Seun Kuti, ya yi kakkausar suka ga rundunar ‘yan sandan Najeriya in da ya ya zarge su da jagorantar kungiyoyin garkuwa da mutane.
Masu zafi
Samu kari