Latest
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya kalubalanci yadda shugaban kasa Bola Tinubu ke rikon sakainar kashi akan tattalin arzikin kasar.
Bayan zaben Sanatoci da aka yi, Musa Mustapha ne zai dare kujerar da Ibrahim Geidam ya bari. Kwamishinan sufurin na jihar Yobe suruki ne ga Ministan ‘yan sanda.
Yadda aka raba ragowar kujerun majalisa tsakanin PDP da APC a Kaduna. A kusan duka zabukan da aka shirya, jam'iyyar LP mai hamayya ce ta rika zuwa ta uku.
An kashe mai shekara 40 ya mutu a wajen zabukan cike gurbi da INEC ta shirya. Mutuwar wannan mutumi a wajen zaben cika gurbin da aka shirya ya jawo zanga-zanga.
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta raba auren wasu yan uwan juna biyu da mahaifinsu ya aurawa malaminsa su a lokaci guda. Malamin da aka aura masu yana a kasar Nijar.
Tsohon gwamnan jihar Yobe, Bukar Abba Ibrahim, ya yi bankwana da duniya yana da shekara 73. Tsohon gwamnan ya rasu ne a kasar Saudiyya inda yake jinya.
Daya daga tsoffin shugabannin hukumar DSS ya bayyana yadda ya ga abin da ya gani a wurin 'yan bindiga. Ya ce ya daina sukar masu biyan kudin fansa a yanzu.
'Yan sanda a Indiya sun tsare wani tantabara na tsawon wata takwas a hannunsu bisa zarginta da yi wa China leken asiri, daga bisani an saki tantabara bayan bincike.
Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta saki sabbin zafafan hotunanta a dandalinta na soshiyal midiya. Wasu na ganin sam shigarta bata dace ba.
Masu zafi
Samu kari