Kujeru 13 da Jam’iyyun APC, PDP da YPP Suka Lashe a Zaben 'Yan Majalisar Tarayya

Kujeru 13 da Jam’iyyun APC, PDP da YPP Suka Lashe a Zaben 'Yan Majalisar Tarayya

  • Jam’iyyar APC ta fi kowa tashi da kujeru masu yawa da aka gudanar da zaben cika gurbi a jihohi
  • PDP mai hamayya ta samu kujerun majalisar wakilan tarayya a jihohin Kaduna, Sokoto da Jigawa
  • APC za ta cigaba da wakiltar mutanen mazabun Dandi/Arewa da Yauri/Shanga/Ngaski a Kebbi

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Mun tattaro kujerun da jam’iyyu suka tashi da suka da aka yi zaben makon jiya:

Majalisa
An yi zaben cike guraben Majalisar tarayya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

1. Fuad Laguda (APC)

Tazarar fiye da kuri’a 10, 000 ne tsakanin Fuad Laguda da duk wani wanda ya yi takara a Surulere a jihar Legas. ‘Dan takaran APC ya samu kuri’u 11, 203.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Adadin kujerun APC a Majalisa ya bayyana da surukin tsohon Sanata ya zama Sanata

2. Garba Umar (APC)

A Yauri/Shanga/Ngaski, Daily Trust ta ce Garba Umar ya samu kuri’u 54,885 wanda ya zo na biyu a zaben shi ne Garba Hassan na PDP mai kuri’u 16,652.

Garba Umar zai maye gurbin Tanko Yusuf Sununu da ya zama Ministan ilmi.

3. Garba Kamba (APC)

Abdullahi Umar-Kamba na PDP ya samu kuri’u 31,858 a zaben da aka yi a Dandi/Arewa, Garba Kamba na APC da ya ci kuri’u 32, 432 ya lashe takarar.

4. Ifeoluwa Ehinderon (APC)

Ana da labarin yadda Ifeoluwa Ehindero ya lashe zabe da ratar kuri’u sama da 20, 000. Yaron tsohon IGP din zai gaji Ministan gida, Olubunmi Tunji-Ojo.

5. Shehu Dalhatu Tafoki (APC)

Shehu Dalhatu Tafoki (APC) zai wakilci mutanen Kankara/Faskari/Sabuwa a majalisar wakilai, ya doke Mohammed Jamilu (PDP) da ratar kuri’u 740.

6. Peter Uzokwe (YPP)

YPP tana da karfi a Anambra har yanzu domin ta doke APGA ta lashe kujerar Nnewi a majalisar tarayya, za a rantsar da Peter Uzokwe mai kuri’u 25, 518.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisar da kotu ta tsige ya haye, APC ta doke PDP da kuri’u 600

7. Chinwe Nnabuife (YPP)

Jam’iyyar ta YPP ta samu karin kujerar majalisar tarayya a shiyyar Orumba ta Arewa da Kudu. Rahoton ya ce Chinwe Nnabuife yana jiran rantsuwa ne.

8. Adamu Yakubu (PDP)

Vanguard ta kawo rahoto cewa PDP ta doke APC a zaben da aka yi a mazabar Birnin Kudu/Buji, Adamu Yakubu ya sha gaban Da’u Magaji Aliyu (APC).

9. Muhammad Buba Jajere (PDP)

A Fika/Fune PDP ta samu galaba ta hannun Muhammad Buba Jajere mai kuri’a 32, 557, ya doke Muhammad Aliyu S/Kasuwa da ya samu kuri’u 31,959.

10. Umar Yusuf-Yabo

Duk da APC ke mulki a Sokoto, Umar Yusuf-Yabo na jam’iyyar PDP zai samu wakiltar Yabo-Shagari a sakamakon doke Dan-Bukari mai kuri’a 26, 213.

11. Hussaini Muhammad Jalo

APC ta gaza tsaida Hussaini Jalo, zai cigaba da rike kujerarsa na ‘dan majalisa mai wakiltar Igabi. ‘Dan takaran APC watau Zayyad Ibrahim ne ya zo na biyu.

Kara karanta wannan

Aikin gama ya gama: Dan takarar PDP ya sha kaye a zaben cike gurbi a Yobe, an fadi wanda ya lashe

12. David Jesse

David Jesse da ya yi takara a APC ya ci kuri’u 18, 566, ya doke Maria Dogo da Solomon Adamu na jam’iyyun PDP da LP a mazabar Chikun ta tarayya a Kaduna.

13. Daniel Asama Ago

‘Dan takaran LP ne ya ci zaben ‘dan majalisar Jos ta Arewa da Bassa. Daniel Asama Ago ya doke jam’iyyun ADC, NNPP, PRP da APC mai mulkin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel