Latest
Tsohon dan takarar shugaban kasa kuma lauya, Cheif Reuben Famuyibo, ya gargadi shugabannin Arewa da su daina cusa ƙiyayyar Shugaba Tinubu a zukatan 'yan Najeriya.
Yayin da ake cikin wani hali a Najeriya, Majalisar Dattawa ta yi alƙawarin tsayawa don tabbatar da ba a kara farashin mai da wutar lantarki ba a kasar.
An kama Umar Hashim, Edidiong Umoh, Udah Stanley, Abubakar Jariri da Yunusa Babangida da zargin satar abinci. An yi nasarar gano buhuna 1, 238 daga cikin buhunan.
Cibiyar kula da cututtuka ta Jihar Kebbi (EOC), ta sanar da jama’a game da bullar cutar murar tsuntsaye a wasu sassa na jihar kuma har kashe tsuntsaye a Amanawa.
Bayan ganawa da masu siminti a Najeriya kan tsadar siminti, kungiyar masu sarrafa ta sun yi alkawarin daidaita farashin siminti amma da sharadi ga Gwamnatin Tarayya.
Tun da Bola Tinubu ya karbi rikon Gwamnatin Najeriya karin wahala da kuncin rayuwa ake ta shiga. Sanata Sani Musa ya nuna cewa tsare-tsaren APC ba su aiki.
Mai ajiyar kudi ta jam'iyyar Labour Party da aka dakatar, Misis Oluchi Opara, ta sake taso shugaban jam'iyyar a gaba kan zargin karkatar da kudaden jam'iyyar.
Gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ta fara biyan albashin malaman jami'o'i na kungiyar ASUU da aka rike saboda yajin aikin da suka yi.
Yayin da ake zargin shugaban sansanin Bama da ke jihar Borno, Abbah Tor da karkatar da wasu kayayyaki, Gwamna Zulum ya fatattake shi daga sansanin.
Masu zafi
Samu kari