Latest
Bankin duniya ya kafawa Najeriya manyan sharudda kafin ya ba ta rancen dala biliyan 1.5. Bankin Duniya ya ce zai iya soke rancen kudin idan aka karya dokokin.
An samu bullar cutar kwalara a jihar Legas inda ta kashe mutane sama da 21 sannan ta kwantar da mutane sama da 400. Gwamnati ta ce suna kokarin shawo lamarin.
Wasu matasa sun yi ajalin wani mai suna Yunusa wanda ɗan Faira ne kan zargin furta kalamai marasa daɗi ga Annabi Muhammad (SAW) a Bauchi da ke Aewacin Najeriya.
Wata babbar kotun jihar Ondo da ke zama a Akure ta yi watsi da kananan hukumomi 33 da gwamnatin marigayi tsohon Gwamna Oluwarotimi Akeredolu ta kirkiro.
Kotun ɗaukaka kara mai zama a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers ta tanadi hukuncinta kan rigimar dauya shekar ƴan majalisa 27 da ke marawa Wike baya.
Wasu masu zanga-zanga sun dira gidan gwamnatin jihar Kaduna. Sun bukaci gwamnan jihar, Uba Sani, ya cafke magabacinsa Malam Nasir Ahmad El-Rufai.
Hukumar FIU ta kasar India ta lafta tara kan kamfanin hada-hadar kirifto na Binance kan zargin safarar kudade. Hukumar ta ci kamfanin tarar Dala miliyan 2.25.
Gwamnatin India ta sanar da mutuwar mutane 36 da kuma sama da 100 da ke wance a asibiti bayan shan giya a yankin Kallakurichi da ke jihar Tamil Nadu.
Babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta sanar da cewa za ta ci gaba da zaman shari'ar kan rigimar sarautar Kano da misalin karfe 2:00 na rana yau Alhamis.
Masu zafi
Samu kari