Latest
Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf ya lashi takobin kwato hakkin mutanen da suka mutu da wadanda suka jikkata a harin bam da aka kai masallacin Gezwa da ke jihar.
Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta samu nasarar rage mugun iri bayan ta hallaka 'yan bindigan da suka addabi jama'a. An kuma kwato makamai a hannunsu.
Rahoto ya bayyana yadda sojoji suka ceto wasu mutanen da aka sace tsawon shekaru 10 da suka wuce a cikin dajin Sambisa da ke jihar Borno a Arewacin Najeriya.
An tabbatar da rasuwar shugaban kasar Iran, Ebrahim Raisi da wasu jami'an gwamnatin kasar a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu da ya ritsa da su.
Kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen ya bukaci shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya warware rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar..
Jama'ar jihar Imo sun shoga tashin hankali bayan da babbar mota ta murkushe kananan motoci bas hudu tare da kashe mutane da dama ana tsaka da zama.
'Yan sanda sun kama Nze Chinasa Nwaneri, tsohon mai baiwa Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo shawara kan ayyuka na musamman a wani otel da ke Owerrri.
Shugaba Tinubu ya nada Ajuri Ngelale wakilin shugaban kasa na musamman kan ayyukan sauyin yanayi da kuma sakataren kwamitin mutane 25 da aka kafa kan shirin GEI.
Rundunar 'yan sanda a jihar Akwa Ibom ta tabbatar da sace basarake, Ogwong A Abang a jihar a daren jiya Asabar 18 ga watan Mayu bayan sun kutsa kai cikin fadarsa.
Masu zafi
Samu kari