Latest
Tsaren-tsaren CBN na ci gaba da ɗaga kimar kuɗin Najeriya yayin da Dalar Amurka ta kara karyewa a kasuwar hada-hadar gwamnati ranar Talata, 21 ga Mayu.
Sanata Garba Maidoki ya yi iƙirarin cewa a kowane wata Gwamna Nasiru Idiris na bai wa sojoji N500m domin su yi aikin tabbatar da tsaron al'umma a faɗin Kebbi.
Biyo bayan kashe mutum 50 da yan bindiga suka yi a garin Zurak da ke karamar hukumar Wase a jihar Filato, an kara samun mutum shida da suka mutu.
Ministan kasafi da tsare-tsare a Najeriya, Atiku Bagudu ya fito fili ya ba ƴan kasar hakuri kan halin kunci da ake ciki inda ya kare matakan da Bola Tinubu ke dauka.
Mahaifi ya kai dansa kara kotu a Kano saboda matsalar sata da shaye-shaye, ya bukaci alkalin kotun ya masa daurin rai da rai. Kotun ta daga shari'ar zuwa watan Yuni.
Jami'an hukumar DSS da ƴan sanda sun kai ɗauki zauren majalisar dokokin jihar Kuros Ribas bayan ƴan majalisar sun tsige shugaba kan zargin almundahana.
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba tsohon dan sanda, DCP Abba Kyari belin makwanni biyu yayin da yake jimamin mutuwar mahaifiyarsa a jihar Borno.
Tsohon Shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa akwai bukatar shugabannin kasashen Afrika su sake duba na tsanaki kan dimukuradiyya.
Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana abubuwan da ke kawowa mata cikas a siyasar Najeriya.
Masu zafi
Samu kari