Murna Yayin da Farashin Dala Ya Ƙara Karyewa a Kasuwar Hada Hadar Kudi a Najeriya

Murna Yayin da Farashin Dala Ya Ƙara Karyewa a Kasuwar Hada Hadar Kudi a Najeriya

  • Ƙimar Naira ta ƙara sama a kasuwar hada-hadar gwamnati ranar Talata sa'o'i 24 bayan kuɗin Najeriya sun rikita Dalar Amurka
  • Rahoton FMDQ ya nuna cewa Naira ta tashi da N3.31 inda aka yi musayar kowace Dalar Amurka kan N1,465.68
  • Shugaban kungiyar ƴan kasuwar cinikayyar kudi, Aminu Gwadabe, ya yabawa CBN da sauran hukumomin tsaro bisa matakan da suka ɗauka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ga dukkan alamu Naira ta ƙara yunƙurowa a kasuwar hada-hadar kudi a lokacin da Dalar Amurka ke ƙara karyewa.

A ranar Talata, 21 ga watan Mayu, Naira ta farfaɗo da N3.31 a kasuwar gwamnati inda aka yi musayar kuɗi kan farashin N1,465.68/$.

Kara karanta wannan

"Dalilin da ya sa Kwankwaso, Atiku da Peter Obi ba za su kai labari ba a zaɓen 2027"

Naira da Dala.
Darajar Naira ta ƙaru a kasuwar gwamnati ranar Talata Hoto: Contributor
Asali: Getty Images

Bayanai daga hukumar kula da musayar kuɗi FMDQ sun nuna cewa ƙimar Naira ta ƙaru da kaso 0.22% a kasuwa idan aka kwatanta da farashin ranar Litinin, The Nation ta ruwaito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta tattaro muku cewa a ranar Litinin, 20 ga watan Mayu, farashin Dalar Amurka ya karye zuwa N1,468.99.

Bugu da ƙari, an samu ƙarin yawan Dalolin da aka yi hada-hadarsu ranar Talata, inda adadin ya ƙaru zuwa Dala miliyan 268.17 daga $161.41m da aka yi cinikayyar su ranar Litinin.

Ana ganin dai hakan na da alaƙa da matakan da babban bankin Najeriya (CBN) ke ci gaba da ɗauka domin dadaita kasuwar musayar kuɗi a Najeriya.

ABCON ta yabawa CBN da hukumomin tsaro

Kungiyar ƴan canji ta Najeriya (ABCON) ta yabawa CBN bisa tsare-tsaren da ya kawo wanda ke ƙara wa Naira daraja a kasuwar gwamnati, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Ministar Tinubu ta ware N290m domin samar da fitilu a karamar hukumarta

Shugaban ABCON, Aminu Gwadabe, ya bukaci CBN ya ci gaba da aiwatar da irin waɗannan tsare-tsaren da za su ɗaga ƙimar kuɗin mu na gida Najeriya.

Gwadabe ya alaƙanta farfaɗowar Naira da kokarin da gwamnati ke yi da kuma matakan da wasu hukumomin tsaro suka ɗauka.

"Ina farin cikin yadda hukumomi da dama suka haɗu domin tunkarar wannan ƙalubale," in ji Gwadabe.

CBN ya soke harajin yanar gizo

A wani rahoton kun ji cewa babban bankin Najeriya CBN ya kara kuɗin ruwa daga 24.75% zuwa 26.25% wanda ya kasance karo na uku kenan a cikin wannan shekara.

Hakan na zuwa ne bayan soke biyan harajin yanar gizo da bankin ya yi niyyar ƙaƙabawa ƴan Najeriya bayan korafe-korafe da ake ta yi a kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel