Atiku Ya Bayyana Matsayarsa Kan Takarar Shugaban Ƙasa a 2027, an Yaɗa Bidiyo

Atiku Ya Bayyana Matsayarsa Kan Takarar Shugaban Ƙasa a 2027, an Yaɗa Bidiyo

  • Ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar ya magantu kan tsayawa takara a 2027
  • Atiku ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a zaben 2027 a cikin wani faifan bidiyo a yau Laraba 22 fa watan Mayu
  • Legit Hausa ta tattauna da ɗan a mutun Atiku Abubakar kan wannan mataki da dan takarar ya dauka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a 2027.

Atiku Abubakar ya tabbatar da haka ne a yau Laraba 22 ga watan Mayu yayin hira da 'yan jaridu.

Atiku ya ce zai sake tsayawa takara a zaben 2027
Atiku Abubakar ya bayyana cewa zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2027. Hoto: Atiku Abubakar.
Asali: Facebook

Atiku ya magantu kan takarar 2027

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu Ado: Atiku ya yi magana kan rikicin sarautar Kano, ya fadi mai laifi

Jigon PDP, Abdul'aziz Na'ibi Abubakar ya tabbatar da haka a shafinsa na X tare da wallafa faifan bidiyon.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai Atiku bai bayyana wanda zai yi masa mataimaki ba a zaben 2027 yayin hirar da ya gabatar.

"Abin farin ciki ga duk ƴan Najeriya yayin da Atiku Abubakar ya tabbatar zai tsaya takara a zaben 2027."
"Shin kun shirya zabensa a 2027?"

- Abdul'aziz Na'ibi Abubakar

Ganawar Atiku da Obi kan zaben 2027

Ɗan takarar shugaban kasar ya bayyana haka kwanaki kadan bayan ganawa da takwaransa na LP, Peter Obi.

Ana ta jita-jitar cewa wannan ganawa na da alaƙa da hadin kan jam'iyyun adawa domin neman kwace mulki a hannu APC.

Sai dai jami'yyar APC ta yi fatali da shirin hadakar da ake magana inda ta ce ita inganta rayuwar al'umma ne a gabanta.

Kara karanta wannan

"Dalilin da ya sa Kwankwaso, Atiku da Peter Obi ba za su kai labari ba a zaɓen 2027"

Legit Hausa ta tattauna da ɗan a mutun Atiku Abubakar kan wannan mataki da dan takarar ya dauka.

Kwamred Aliyu Abdulkadir Abubakar ya ce ana ihu matasa matasa inda ya ce babu mai kwarewa kamar Atiku.

"Ana ta maganar matasa, a cikinsu babu wanda ya kai Atiku kwarewa da sanin abubuwa da dama a kasar."
"Irinsu Atiku ne za su inganta tsaro da tattalin arziki fiye da matasan da ake magana, kamar su Yahaya Bello da suka tafka barna shi ma ai matashi ne."

- Aliyu Dyer

Aliyu Dyer ya ce dukkan matasan neman cimma muradunsu za su yi ba kamar su Atiku da suke da arzikinsu tuntuni ba, inda ya ce a wurinsa, Atiku yafi matasa 100 ƴan Najeriya."

Atiku ya magantu kan siyasarsa a Najeriya

A wani labarin, an ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa ba zai yi ritaya daga siyasa ba muddin yana raye.

Kara karanta wannan

Tattaunawar hadakar Atiku Abubakar da Peter Obi ta fara daukar hankalin APC

Atiku ya bayyana cewa duk mai tunanin wata rana zai bar siyasa ya koma gefe yana kallo ana zaluntar talakawa to bai ma san abin da yake yi ba.

Dan takarar PDP ya ce duk wanda ke mafarkin cewa zai jingine siyasa a yanzu to ya daina domin shi da siyasa mutu ka raba ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel