Da Sake: Tsohon Shugaba Obasanjo ya Nemi Duba Tsarin Dimukuradiyya a Afrika

Da Sake: Tsohon Shugaba Obasanjo ya Nemi Duba Tsarin Dimukuradiyya a Afrika

  • Dattijon kasa kuma tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bayar da shawarar sake duba kan tsarin dimukuradiyyar da aka gada daga Turai
  • Cif Obasanjo ya bayyanawa taron masu ruwa da tsaki kan halin da dimukuradiyya ke ciki a babban birnin tarayya Abuja cewa dole a kula da shugabanci na gari
  • Ya jaddada cewa dimukuradiyya tsari ne da ya kamata a kakkabe cin hanci da rashawa a cikinsa, tare da neman shugabannin su yi mulki da adalci da ya dace da 'yan Afrika

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa akwai bukatar shugabannin kasashen Afrika su sake duba na tsanaki kan dimukuradiyyar da aka gada daga turawa.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta haramta nuna tsafin kudi a fina finan 'Nollywood'

Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa dole ne sai shugabanni sun samar da wani tsarin dimukuradiyya da zai dace da tsarin rayuwar ‘yan Afrika.

Olusegun Obasanjo
Tsohon Shugaba Obasanjo ya nemi a sake duba kan tsarin dimukuradiyya Hoto: Leigh Vogel
Asali: Getty Images

Channels Television ta wallafa cewa Olusegun Obasanjo ya bayyana haka ne yayain taron halin da dimukuradiyya ke ciki a cibiyar taro na Yar’adua dake Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya nanata cewa kamata ya yi a samar da tsarin dimukuradiyyar da zai tafi da bukatun dukkanin ‘yan Afrika.

Obasabjo ya nemi a gyara dimokuradiyya

Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya shawarci shugabannin Afrika su dage wajen tallafawa mutanen da suke wakilta.

Vanguard News ta wallafa cewa matukar ana son dimukuradiyyar da kowa zai mora, sai an dora ta a tsarin gaskiya da shugabanci na gari.

Ya bayyana cewa babu cin hanci da rashawa a tsarin dimukuradiyyar gaskiya, matukar za a wakilci al’umma yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

"Yadda Tinubu ya bi ya hana tattalin arzikin Najeriya durkushewa", Kashim Shettima

An gano 'kuskure' a tsarin mulkin Najeriya

A baya mun kawo muku labarin cewa wasu daga cikin 'yan majalisa sun fara kokarin kawo sauyi cikin kundin tsarin mulkin Najeriya bayan gano kura-kurai a cikinsa.

Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa akwai kura-kurai a tsarin mulkin kuma ya kara da cewa akwai abubuwan da 'yan majalisa ya dace su fi mayar da hankali a kai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel