Tijjani Gandu Ya Fadi Gaskiyar Alakar da Ke tsakaninsa da Jaruma Maryam Booth
- Bayan ce-ce-ku-cen da aka samu a kafofin sadarwa na zamani, Tijjani Gandu ya fito fili, ya fadi alakar da ke tsakaninsa da jaruma Maryam Booth
- Fitaccen mawakin ya ce shi da Maryam sun dauki wasu hotuna da suka jawo rudani a yanar gizo har lamarin ya so ya wuce gona da iri
- A wata tattaunawa da aka yi da shi, Tijjani Gandu ya ce dama can ya san Maryam, tare da fadin gaskiyar abin da ya sa suka yi hotunan
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Shahararren mawaƙin siyasa, Tijjani Gandu ya fito fili, ya fadawa duniya gaskiyar alaƙar da ke tsakaninsa da jarumar Kannywood, Maryam Booth.
Wannan na zuwa ne bayan da wasu hotunan Tijjani Gandu tare da Maryam Booth masu kama da na aure suka yaɗu kamar wutar daji a soshiyal midiya.

Source: Facebook
Tijjani ya yi martani kan hotuna da Maryam Booth
Tijjanin Gandu, wanda kuma shi ne mai ba gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf shawara kan al'adu, ya shaida wa TRT Afrika Hausa gaskiya game da alakarsa da Maryam Booth.
A hirar da suka yi ta wayar tarho, Tijjani ya bayyana cewa:
"Zan yi bayanin abubuwan da suka faru satin da ya gabata, kasancewar ganin hotuna na da Maryam Booth, abokiyar aiki. Wadannan hotunan sun jawo ce-ce-ku-ce.
"Har yanzu wasu ba su gane gaskiyar wannan lamari ba. Na ga ya dace, kamar yadda kuka tambaya, in yi maku bayani.
Mawaki Tijjani Gandu ya bayyana cewa shi wannan lamari, watau hotunan da aka ga ya dauka da Maryam Booth, aiki ne suka yi na waka da jarumar.
Dalilin ganin hotunan Maryam Booth da Tijjani Gandu
Fitaccen mawakin, ya bayyana dalilin da ya sa ya dauki hotunan da suka yi kama da na kafin aure da jaruma Maryam Booth, yana mai cewa:
"Shi wannan aiki ne muka yi, aiki irin na waka, kasancewata mawaki, bangare-bangare, to wannan waka ce aka yi ta 'Amarya Mai Capacity,' muke so mu fito da bidiyonta ta wani irin salo, shi ya sa muka shirya wannan.
"Kuma an dauki wadannan hotuna ne da ku ke gani suna yawo a lokacin da aka dauki wannan waka, kuma hotunan aka fara saki. An yi abin ne saboda raha, a dan ja hankali, to sai kuma abin yake nema ya wuce gona da iri."
Mawakin ya jaddada cewa an dauki hotunan ne kawai saboda aiki, kamar yadda aka saba ganin jaruma da jarumi suna yi don tallata wani bidiyo ko fim da za su saki.

Source: Facebook
Alakar Tijjani Gandu da Maryam Booth
Game da jita-jitar da wasu ke yadawa, cewa Tijjani Gandu zai auri Maryam Booth ne, shi ya sa suka yi wadannan hotunan, mawakin ya ce ko kusa ba haka ba ne.
"Masu tambayar me ya sa ba a dauko wasu jarumai ba, aka dauko ita Maryam Booth, to kasancewar idan za ka yi aiki, kana duba yiwuwar wa ya fi cancanta ka dauko, ko kuma waye zai ba ka abin da kake nema, shi ya sa muka dauko wannan jaruma.
"Baya ga haka, kamar yadda ku ke gani, ita jarumar ta ba da yanayin abin da ake bukata. Masu tambaya cewa kuma muna da wata alaka ne ta soyayya, ko kuma dama can mun san juna, to maganar gaskiya dama can mun san juna amma babu wata alaka ta soyayya da ke tsakaninmu."
- Mawaki Tijjani Gandu.
Kalli bidiyon tattaunawar a nan kasa:
Martanin ƴan Najeriya kan kalaman Tijjani Gandu
Legit Hausa ta tattauna da wasu masu bibiyar masana'antar Kanywood don jin ta bakinsu game da bayanin Tijjani Gandu.
Bashir Khalid Furyam daga jihar Bauchi ya ce:
"Bayanin da Tijjani Gandu ya yi kan hotunan shi da Maryam Booth ya yi dai dai da tunani na. Ni dama na ce ba soyayya ko aure za su yi ba, kawai dai wata salon talla ce.
"A masana'antar nishaɗi irin Kanywood, ko waka, ana amfani da irin wadannan hotunan masu kama da na aure don jawo hankalin jama'a.
"Ni dai shawara ta ita ce Tijjani Gandu ya gaggauta fitar da wakar nan don ya riga ya rikita soshiyal midiya. Idan ya jinkirta, jama'a za su manta, don haka akwai buƙatar cin moriyar wannan tallar da wuri."
Shi kuwa Abba Hassan Gezawa daga Kano cewa ya yi:
"Malam Sani, ka san ita harkar nan tamu sai da irin haka, dole ka dan yamutsa hazo don ka samu abun da kake so. Kuma lallai Tijjani Gandu ya samu abun da yake so.
"Ka san shi dam Tijjani akwai shi akwai son kawo wani abu sabo, kuma cikin nasibinsa, idan ya kawo abu to sai ya shahara.
"Ina fatan waƙar 'Amarya Mai Capacity' za ta yi kyau kuma ta cancanci duka wannan tallar da aka yi mata a yanzu."
Amina Lawal daga Funua ta ce ta yi mamakin ganin hotunan Tijjani Gandu da Maryam Booth, a cewarta, ita ta dauka da gaske aure ne za su yi.
"Ina daga cikin wadanda suka rika taya su murna, har ina cewa ai kuwa sun dace, ashe ashe dai kawai wasa ne. Na ji haushi da na zo na fahimci waka ce kawai suka yi tare.
"Ni dai ina gain bai kaata a rika mayar da wannan abun ya zama hanyar yaudarar jama’a ba domin cimma burin kai. Don a lokacin na ji ana cewa kamar ya yaudari wata mawakiya ta fito tana maganganu."
- Amina Lawal.
'Na gaji da tambayoyi kan aure' - Maryam Booth
A wani labari, mun ruwaito cewa, jaruma Maryam Adamu wacce aka fi sani da Maryam Booth ta magantu a kan yawan tambayar da ake yi mata na 'yaushe za ki yi aure?."
Maryam Booth ta ce shi aure nufi ne na Ubangiji, kuma duk yadda mutum ya kai ga shirin aure idan Allah bai yi lokacin nan ba toh babu yadda za kayi.
Hakazalika, jarumar ta koka kan yadda mutane ke yawan tambayar ta dalilin da ya sa ta rame, tana mai cewa, mutuwar mahaifiyarta ta gigita ta sosai, don haka dole ta rame.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng




