Wasiyyar da Mahaifinsu Rahama Sadau Ya Bari kan Auren Ƴaƴansa kafin Ya Rasu
- Yayan Rahama Sadau da ke kira Haruna Ibrahim ya tabbatar da daura auren ta a Kaduna yau Asabar 9 ga watan Agusta 2025, da sadaki N300,000
- Mutumin da aka fi sani da Abba Sadau ya bayyana cewa wasiyyar mahaifinsu ta ƙarshe ita ce auren yayansa mata
- Ya ce mijin Rahama mai suna Ibrahim ba dan Kannywood ba ne, kuma ba a sako hotonsa ba saboda iyalansu sun ɓoye labarin auren ne
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Daya daga cikin yan uwan Rahama Sadau ya yi karin haske kan batun auren jarumai da aka yi a Kaduna.
Haruna Ibrahim wanda aka fi sani da Abba Sadau wanda yaya ne ga Rahama ya tabbatar da daura auren a yau Asabar 9 ga watan Agustan 2025.

Source: UGC
Wasiyyar mahaifin Rahama Sadau kafin rasuwarsa
Hakan na cikin wata hira da jaridar DCL Hausa ta wallafa a shafin Facebook inda Abba ya fadi yawan sadaki da aka biya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin hirar, Abba ya ce an biya sadakin N300, 000 domin tabbatarwa da kuma shaida daurin auren.
Ya ce kafin rasuwar mahaifinsu babban burinsa shi ne su yi aure domin shi ne martabar yara mata.
Nawa ne sadakin auren Rahama Sadau?
Abba ya ce Allah ya ƙaddara har ya rasu hakan bai faru ba inda su kuma matan suka yi alkawarin cika masa burinsa bayan rasuwarsa.
Ya ce:
"Eh ta yi aure, a cikin wasiyyar da babanmu ya bari shi ne maganar aurar da yayansa kafin ya rasu.
"Tun lokacin kowacce ta yi alkawarin idan aka yi sadakar arba'in za ta fito da miji ta yi aure, sai aka fara babbar.
"Yau kwana 10 kenan da yin arba'in dinsa shi ne aka fara da na Rahama, kuma an ba da sadaki N300,000."

Source: UGC
Wanene mutumin da ya auri Rahama Sadau?
Abba Sadau ya kuma yi magana kan mijin da Rahama Sadau ta aura inda ya ce ba a sako hotonsa ba amma kuma ba dan Kannywood ba ne.
Ya tabbatar da cewa mafi yawan mutane ba su san da auren ba saboda an boye ne ka da abin ya bayyana har sai dai a ji an daura aure.
Ya kara da cewa:
"Mijin kuma wani bawan Allah ne sunansa Ibrahim ba a fitar da hotonsa ba a hukumance kuma bai cikin harkar fina-finai.
"Yawanci wadanda suke kusa ma ba su sani ba, mu iyalai ne muka san da maganar sai wasu da ba za a rasa ba."
Mahaifin Rahama Sadau ya rasu
A baya, mun ba ku labarin cewa an tabbatar da rasuwar mahaifin jarumar Kannuwood da aka fi sani da Rahama Sadau.
Dattijon ya rasu ne a ranar Lahadi 22 ga watan Yunin 2025 bayan fama da jinya inda jarumai mata da maza suka yiwa iyalan Sadau ta'aziyya.
Majiyoyi suka ce marigayin ya rasu a jihar Kaduna, kamar yadda Rahama ta bayyana a wani saƙo da ga wallafa a kafar sadarwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

