Fitattun Jaruman Kannywood da Suka Yi Suna amma Suka Zama Abin Tausayi daga Baya

Fitattun Jaruman Kannywood da Suka Yi Suna amma Suka Zama Abin Tausayi daga Baya

Kano - A tarihin masana'antar Kannywood an yi wasu fitattun jarumai da suka sanu a Najeriya da wasu ƙasashen ketare.

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

An yi wasu jarumai ciki har da mawaka da suka sheke ayarsu a lokacin da duniya take tare da su a Kannywood kafin daga bisani ta juya musu baya.

Jaruman Kannywood da suka yi suna a baya
Fitattun jaruman Kannywood da duniya ta yi watsi da su bayan shura a baya. Hoto: Kannywood Update.
Source: Facebook

Daya daga cikinsu, Ummi Nuhu ta yi hira da BBC Hausa a kwanakin nan inda take nadamar rayuwarta a baya.

Mafi yawa daga cikin jaruman a yanzu babu wanda yake shiga sabgarsu saboda yadda duniya ta juya musu baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akwai wasu har da mawaka da suka yi tashe amma yanzu ko ganinsu aka yi gudu ake yi saboda yadda rayuwa ta maida su.

Sai dai duk da haka akwai wadanda suka yi suna a baya taurarinsu suka dusashe amma kuma sun dawo ana damawa da su.

Kara karanta wannan

Ana batun sulhu, yaran Bello Turji sun harbe mutane a Sokoto, sun sace mutum 16

Jaruman Kannywood da suka rasa shahararsu

Legit Hausa ta duba wasu daga cikin jaruman da suka samu jarabawar rayuwa:

1. Bashir Bala Chiroki

Bashir Bala Chiroki na daga cikin jaruman Kannywood da suka yi shura a shekarun baya.

Rahotanni sun ce Chiroki ya fara fim ne fiye da shekaru 30 da suka wuce kuma ya yi kaurin suna kafin daga baya rayuwa ta sauya.

Daga bisani a shekarar 2019, Chiroki ya bayyanawa duniya halin da ya shiga da kuma watsi da aka yi da shi a masana'antar.

Ya ce har kunun aya yake sayarwa saboda daraktoci da furodusoshi sun yi watsi da shi ba su taimakonsa a dauke shi aiki.

Dalilin haka, shafin sada zumunta na Instagram (Northern_hibiscuss) ya ba Bashir Bala Chiroki kudi sama da N200,000 a ranar Talata, 22 ga watan Janairun 2019.

Chiroki ya yi jawabin godiya ga shafin Northern_Habiscuss wadda a cewarsa babu na dayansu, ya ce ya gode da Allah ya sa tausayinsa a zuciyoyinsu.

Kara karanta wannan

Ana jita jitar rashin lafiyar Tinubu, Sanata ya fadi halin da Shugaban kasa ke ciki

Sai dai fa a yanzu, Chiroki ya sake dawowa kan ganiyarsa domin a yanzu haka yana cikin fitattun fina-finai masu dogon zango da ake yi.

Chiroki ya dawo kan ganiyarsa a Kannywood
A baya, Chiroki ya koka kan rashin taimaka masa a Kannywood. Hoto: Kannywood Update.
Source: Facebook

2. Ummi Nuhu

Tsohuwar jarumar fina-finan Kannywood, Ummi Nuhu, ta bayyana halin da ta shiga bayan ta ja da baya da fim saboda rashin lafiya.

Ummi ta ce hadari da ta yi ne ya jefa ta cikin mawuyacin hali da har ake tunanin a yanke mata kafa amma likita ya ki yarda.

Jarumar ta ce da za ta iya komawa baya, da ta sauya wasu abubuwa da suka faru, ta kuma ce ba ta so ko maƙiyinta ya shiga irin halin da ta shiga.

Ummi Nuhu ta bayyana yadda rashin karɓuwa ya hana ta komawa harkar fim kuma ta taba burin kawowa Kannywood, amma sau da dama tana jin kamar an manta da ita gaba ɗaya.

Yayin da ta ke bayani kan aure da wasu abubuwa, tsohuwar jarumar ta ce fim ne abin da ta fi iyawa a rayuwarta amma kuma yanzu ba a damawa da ita.

Kara karanta wannan

Sokoto: Ƴan bindiga sun shammaci masallata a sallar isha, sun kashe wasu da dama

Ummi Nuhu ta fadi halin da ta shiga a rayuwa
Ummi Nuhu ta yi nadama yayin da ta yi shura. Hoto: Hadiza Aliyu.
Source: Twitter

3. Aminu Mai Dawayya

Fitaccen mawaki, Aminu Lajawa Mai Dawayya ya bayyana irin nasarorin da ya samu a lokacin da ya yi fice a Kannywood da waka.

Mai Dawayya ya ce a wancan lokaci ya taimaki mutane da dama, kuma babu mawakin da ya yi tashe da bai amfana da shi ba.

Sai dai ya a yanzu kuwa ya ce Allah ya jarrabe shi da rashin arziki, hatta mota ko keke bai mallaka ba, amma yana mai godewa Allah.

Mawakin a kwanakin baya ya sake fitowa har yana zuwa bikin aure ya yi waka tare wasu fitattun mawaka kamar Ado Gwanja wanda asali yaronsa ne da Ali Jita da sauransu.

Aminu Mai Dawayya ya koka kan rayuwarsa a yanzu
Mawaki Aminu Mai Dawayya ya taba shura da ya yi a masana'antar Kannywood. Hoto: Aminu Mai Dawayya.
Source: Facebook

4. Zainab Abdullahi (Indomie)

Zainab Indomie na daga cikin fitattun jarumai da suka yi bajinta a lokacin da suke kan ganiyarsu duba da kyan halitta da Allah ya yi mata.

Indomie ta shigo harkar fim a 2008 da taimakon Adam A Zango kamar yadda ta tabbatar a wata hira da jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Biki bidiri: An daura wa jaruma Rahama Sadau aure a jihar Kaduna

A 2012, Indomie ta samu lambar yabo ta jaruma da ta fi kowa fice a shekarar kafin daga bisani ta bace bat.

An yi ta yada jita-jita cewa ta samu matsala a rayuwa, wasu ko cewa su ke ta mutu kafin daga bisani ta ƙaryata.

Jarumar ta sake dawowa fim a farkon shekarar 2024 tare da taimakon mai gidanta, Adam A Zango inda yanzu take fitowa a wasu fina-finai.

Zainab Indomie ta dawo bayan bata na dogon lokaci
Zainab Indomie tana daga cikin jaruman da suka yi suna a baya. Hoto: Zainab Abdullahi Indomie.
Source: Facebook

Jarumar Kannywood ta fadi silar shiga fim

Mun ba ku labarin cewa jarumar Kannywood, Nusaiba Muhammad Ibrahim wacce aka fi sani da Sailuba, ta ce musuluntar wata ce ya ja hankalinta zuwa fim.

Sailuba a Dadin Kowa ta ce fim yana burge ta tun da farko, amma ganin yadda wani fim ya sa wata ta karɓi Musulunci ne ya ƙarfafa niyyarta.

Nusaiba ta bayyana cewa tana harkar fim kusan shekaru takwas yanzu, kuma tana fatan zama mai bayar da umarni nan gaba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.